Labarai

Nayi alƙawarin tattaki daga birnin Accra zuwa Lagos idan Super Eagles ta doke ƙasar Ghana ayau ~Cewar Jarumi, John Dumelo

Jarumin kaɗe-kaɗe a ƙasar Ghana mai suna John Dumelo yayi alƙawarin yin tattaki daga birnin Accra, Ghana zuwa Lagos, Nigeria idan Super Eagles ta doke ƙasar Ghana a wasan share fage na gasar Kofin Duniya da za’a fafata yau tsakanin ƙasashen biyu.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by John Dumelo (@johndumelo1)


Ayau ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagle zata fafata da ƙungiyar Black Stars ta ƙasar Ghana da misalin ƙarfe 8:00pm a filim wasa na Baba Yara dake Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
Shahararren jarumin, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram. Kamar yadda ya bayyana cewa, “babu yadda za’ayi Nigeria ta samu nasara a wasan yau, idan kuma suka yi nasara, zai yi tafiya ƙafa-da-ƙafa daga birnin Accra zuwa Lagos, Nigeria.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button