Labarai

An jiyo ƙarar harbe-harbe yayin da ƴan sanda su ka mamaye gidan Muhuyi Rimingado a Kano

A jiya da yammacin Lahadi ne dai a ke zargin cewa jami’an ƴan sanda a Jihar Kano sun mamaye gidan tsohon Shugaban Hukumar Ƙorafe-ƙorafen jama’a da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado.
A watan Yulin bara ne a ka dakatar da Rimingado bayan da ya fara binciken zargin badaƙala da aringizon kuɗaɗen kwangiloli da a ke zargin da hannun iyalin gwamna a ciki.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa ƴan sandan sun girke motocin su a kofar gidan Rimingado da ke kan titin Yahaya Gusau, inda da ga bisani su ka dirar masa da misalin ƙarfe 7 na yamma.
Mazauna unguwar sun tabbatar da mamaye gidan Rimingado da ƴan sanda su ka yi ga DAILY NIGERIAN, inda su ka ce sun ji ƙarar harbe-harbe yayin da ƴan sandan ke ƙoƙarin kama shi.
Mazauna unguwar sun ƙara da cews bayan sun ji ƙarar harbe-harben da misalin ƙarfe 7 na yamma, da misalin 9:30 na yamma sai kuma a ka ga motocin su na cin taya yayin da su ka bi wata mota da ta fito da ga gidan Rimingado.
Jaridar ba ta samu tabbacin ko ƴan sandan sun cafke Rimingado a yayin sintirin ba.
Da a ka tambayi kakakin rundunar yan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba a bashi bayani a kan lamarin ba, inda ya yi alkawarin zai bincika.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button