Labarai

An Gano Wata Burdurwa Mai Karyar Gurgunta Tana Bara A Jihar Lagos

Dubun wata matashiyar yarinya da ke karyar gurgunta tare da zama akan keken guragu ya cika a jihar Lagos.

Mutane sun cika da mamaki bayan wasu gungun matasa sun tilastawa wata budurwar yarinya mai karyan gurgunta ta tashi tsaye daga kan keken guragun kuma ya bayyana karara cewa ba gurguwa bace.

An tilasta mata yin tafiya sannan mutanen da ke wajen suka dunga mamakin yadda ta mikye tsaye da kafafunta garas.
Majiyar mu ta labarta mana cewa jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na wata mabaraciya da ta yi ikirarin cewa ita gurguwa ce don kawai ta tara kudi a harkar bara.
Yarinyar na zama ne a kan keken guragu wanda musamman ta tanade shi domin yin wannan harka da kuma yawo a yankin Ikeja tana rokon kudi daga hannun mutane a matsayin mai nakasa.

View this post on Instagram

 

A post shared by Instablog9ja (@instablog9ja)


Lokacin da wasu matasa da suke lura da ita suka kama ta, sai suka tilasta mata sauka daga keken guragun sannan suka sa ta yin tafiya. Tana sauka, sai ya bayyana karara cewa duka kafafuwanta guda biyu lafiya suke babu abun da ya same su.

A wajen da abun ya faru daruruwan mutane sun bayyana matsayar su akan bama almajirar bara inda wasu suka ce bazasu kara bama kowani mabaraci sadaka ba.

Wato jama’a irin wannan sana’ar ta barar karya ta fi karfi a cikin Nijeriya musamman manyan buranan Nijeriya kamar Lagos, Abuja, Kaduna, Kano, Abia, Delta, Enugu da dai sauransu.
Muna rokon ubangiji Allah ya baramu da san zuciya.
– Abubakar A Adam BabankyautaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button