Labarai

Yan Bindiga Sun Kashe Mata Da Yara Kusan 20 Ana Tsaka Da Sallar Juma’a A Kauyukan Zamfara

Yan Bindiga Sun Kashe Mata Da Yara Kusan 20 Ana Tsaka Da Sallar Juma’a A Kauyukan ZamfaraWasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 20, yawancinsu mata da kananan yara a Kananan Hukumomin Bungudu da Tsafe da ke Jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce a harin da aka kai kauyen ’Yar Katsina da ke Karamar Hukumar Bungudu, an kashe akalla mutum 10.kamar yadda aminiyahausa na ruwaito
’Yan ta’addan, wadanda yawansu ya kai kusan 100 sun kai harin ne a kan babura sannan suka sace wasu mutanen, a daidai lokacin da mazauna yankin ke gudanar da sallar Juma’a.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, “Sun zo da yawan gaske a kan babura sannan suka bude wa mutane wuta. ’Yan Sa-kai sun taka rawar gani matuka wajen kai dauki, in ban da haka, da yawan wadanda aka kashe ma ya fi hakan.
Duk Binciken da akayi akan Dcp Abba kyari ba’a sameshi da laifi ba
Najeriya ta zama kasa ta 1 a Afrika da tafi noman shinkafa, inda ta zama ta 14 a duniya
Zamana matar Adam A zango ya jawomin koma baya -Inji tsohuwar matarsa Amina Rani
“Mafi yawan wadanda aka kashe mata ne da kananan yara, kuma su ma maharan an kashe musu mutane,” inji shi.
Shi ma wani mazaunin garin Magami mai suna Babangida, ya shaida wa Aminiya cewa an hangi maharan na kokarin yin hanyar garin Dandundun da mutanen da suka sace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. Pingback: [Bidiyo] Yadda kishiya ta kashe yar kishiyarta saboda zatayi aure – HausaLoaded.Com
  2. Ansace wata yarinya mai shekara 6 bayan kai wani hari a jahar yobe jiya da sape kimaning karpe 10:45 a gujba

  3. Pingback: Sautin Murya] Allura ta tono galma dan majalisa ya bude aiki akan matsalar tsaron sokoto – HausaLoaded.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button