Labarai

[Bidiyo] Yadda Bashin Naira Dubu 10 Ya Sa Wani Ƙaramin Yaro Ya Saci Ƙanwarsa Mai Shekaru 4 A Duniya

[Bidiyo] Yadda Bashin Naira Dubu 10 Ya Sa Wani Ƙaramin Yaro Ya Saci Ƙanwarsa Mai Shekaru 4 A Duniya
Rundunar ƴansanda a jahar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kama wani yaro mai ƙarncin shekaru da zargin satar ɗiyar kawunsa ƴar shekara 4 a duniya.

Kakakin rundunar ƴansandan SP Gambo Isah ne ya gabatar da yaron mai suna Abubakar Abdulbasir yaro da shekara goma sha takwas 18 wanda yake a marabar kankara dake karamar hukumar malumfashi dake jahar katashina ga manema labarai a jiya Juma’a a hedikwatarsu da ke Katsina

Wani mai suna sanusi abubakar ya kawo rahoto ga jami’an yan sanda cewa yarsa ta bata tun ranar sha takwas 18 ga watan junairu yarsa mai suna halimatu yar shekara hudu 4 da haihuwa sunyi duk kokarin da suke amma abin yaci tura.

Daga baya ya samu kiran waya cewa ya kawo naira dubu saba’in N70,000 ko a bartar da yarsa a kasheta da jin haka ya kawo kara wajen yan sanda, yan sanda da sunka kware da bincike da garkuwa da mutane wato ‘anti kidnapping unit’ suka bazama wajen bincike inda kuma sukayi sa’a suna kama wani yaro mai suna Abubakar Abdulbasir dan shekara goma sha 18 da ke marabar kankara a karamar hukumar malumfashi.

Inda yaron yace dalilinnsa na sace kanwarsa  domin ana binshi bashin naira dubu goma N10,000 na wata hula qube da ya saya yake son ya biya.
Ga cikakken bayyanin yaron da manema labarai.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button