Kannywood

Babban goro sai magogin karfe :Sarkar gwal ta Naira miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikarta

Hafsat IdrisA makon da ya gabata ne dai aka yi bikin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris, inda aka mayarwa da jikar sunan ta, wato Hafsat. Sai dai kuma shagalin bikin sunan ya dauki hankula matuka, ganin yadda cewa wani bikin auren ma bai kai taron sunan yawan jama’a ba, musamman jaruman Kannywood mata.
Uwar mai jegon tayi fita ta kece raini da tsadajjen leshi mai dan karen kyau da sarkar gwal da aka yi kiyasin cewa kudin ta ya kai kimanin naira miliyan goma sha daya (N11m).
Kamar yadda labarunhausa sunka ruwaito, shafin labaran Kannywood dake dandalin Twitter ne ya tabbatar da hakan, inda suka wallffa hoton jarumar tare da rubuta:
“Sarkar gwal din da jaruma HAFSA IDRIS tasaka a ranar sunan jikar ta (Hafsa Jnr) ance kudin ta yakai Naira Milyan Goma Sha Daya!
“Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya mana Hafsa karama… Amin!


Jarumai mata da dama sun halarci wannan gagarumin shagalin suna irin su Mansurah Isah, Sameera Ahmad, Aina’u Ade, Sadiya Gyale, da dai sauran su.
Ga kadan daga cikin bidiyon wajen bikin:

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Pingback: Ko 'Yan Kannywood Za Su Kai Karar Mawaki Naziru Kotu Kan 'Bata Musu Suna? - Imam Aliyu Indabawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button