Kannywood

Yajin Aikin Yan Adaidai: Mawaki Rarara ya Fito da Motoci Domin Daukar Mutane Kyauta a Kano

Yajin Aikin Yan Adaidai: Mawaki Rarara ya Fito da Motoci Domin Daukar Mutane Kyauta a KanoSakamakon yajin aikin masu Adaidaita sahu a jihar kano, shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bada umarnin fito da motocin kungiyarsa ta kwallon kafa domin su rika daukar mutane kyauta.

Kadaura24 ta rawaito al’umma da dama suna ta faman tafiyar kasa sakamakon yajin aikin da ‘yan adaidaita sahu suka fara yi tun a ranar litinin din data gabata.Yajin Aikin Yan Adaidai: Mawaki Rarara ya Fito da Motoci Domin Daukar Mutane Kyauta a Kano

Cikin wani bidiyo da mawakin ya wallafa a shafin kamfaninsa yace Motocin an fito da Motocin ne domin taimakawa al’umma sakamakon mawuyacin halin da suka shiga saboda yajin aikin yan adaidaita sahu.

” An fito da Motocin ne domin su dauki mutane musamman dalibai da zasu tafi ko zasu koma gida kuma kyauta ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba”. Inji RararaYajin Aikin Yan Adaidai: Mawaki Rarara ya Fito da Motoci Domin Daukar Mutane Kyauta a Kano

Al’umma da dama dai suna wahala sosai sakamakon yajin aikin yan adaidaita sahu, wanda ya faru sakamakon rashin fahimtar data shiga tsakanin Hukumar Karota da Yan adaidaita sahu.
One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?