Kannywood

Matan kannywood sunfi mazan kannywood yawan kasuwanci – sadiya kabala

Matan kannywood sunfi mazan kannywood yawan kasuwanci - sadiya kabala
Sadiya kabala

A baya-bayannan, kasuwanci shi ne babban abin da da dama daga matan Kannywood suke runguma a lokacin da suke cikin harkar fim din, ko kuma idan sun bar harkar fim.

Duk da yake su ma mazan Kannywood din suna kasuwanci, amma matan sun fi mazan da ke kasuwanci yawa.

A wannan hirar da BBC, daya daga matan na Kannywood wacce a yanzu ta ja baya da harkar fina-finan Sadiya Kabala ta ce neman makoma da neman tsira da mutunci ne ke sa matan rungumar kasuwanci.

Ta ce a baya matan Kannywood ba su fiya damuwa da neman wata sana’a ba bacin harkar fina-finai, abin da ya sa wasunsu ke shiga halin ka-ka ni-ka-yi idan sun bar harkar fim din.

To sai dai Sadiyan ta ce suna fuskantar babban kalubale inda masu karbar kayansu bashi suke kokarin kassara su.

Ga hirar nan ku saurari karin bayyani.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?