Kannywood

Akwai Wata Maƙarƙashiyar Da Ake Ƙullawa Ƴan ‘A Daidaita Sahu’ Na Ganin Bayan Su a Kano – Cewar Mawaƙi Rarara

Yayin tattaunawar sa da tashar NAGUDU TV game da dambarwar da ke faruwa tsakanin Hukumar KAROTA da kuma ta matuƙa baburan A DAIDAITA SAHU na Kano, fitaccen mawaƙin Siyasa a Najeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi sukuwar Sallah a kan Shugaban Hukumar ta Karota; Baffah Babba Ɗan Agundi dangane da takurawa da uzurawar da ya ke yi wa ƴan A Daidaita Sahu a Kano wadda ya ce hakan ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba.

Domin kamar yadda Rararan ya bayyana, Ɗan Agundi, ba ya isarwa da Gwamna Ganduje labarin halin da al’umma ke ciki game da halin takura da wahalar da su ke ciki a dalilin wannan yajin aikin da ƴan Adaidaitan su ke yi.

Wanda wannan ya sa ya ɗauki nauyin tura motocin sa har guda 7 kan titunan birnin Kano don sauƙaƙawa al’umma wahalhalun da su ke ciki.

Ga dai cikakkiyar hirar ta mu da shi wanda za ku iya saurara ta nan

 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?