Addini

Shaye-shaye na janyo a yiwa mutum azaba ranar lahira — Dr Bashir Aliyu

 
Babban limamin Masallacin Juma’a na Alfurqan a Jihar Kano, Dakta Bashir Aliyu ya baiyana cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na sanyawa a yi wa mai ta’ammali da su azaba a ranar lahira.
Malamin ya ƙara da cewa, a Musulunci, Allah Ya haramta shan kayan maye kuma Ya yi hani ga cinikin su.
Ya kuma baiyana cewa shan miyagun ƙwayoyi na gusar da hankali da lafiyar jikin ɗan’adam.
Dr Aliyu ya baiyana haka ne lokacin da ya ke huɗubar sallar juma’a a masallacin Alfurqan da ke Alu Avenue, Jihar Kano a ranar Juma’a.
Malamin ya yi kira ga hukumomi da su tashi tsaye wajen yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi a tsakanin alumma.
A cewarsa, jihohin Kano da Kaduna da kuma Katsina na cikin manyan jihohin da ake samun rahoton shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran dangin kayan maye.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da kuma Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA da su tashi tsaye wajen kawar da kayan maye a tsakanin alumma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button