Kannywood

Sarkin waka ya ƙara fito da Hujjar tafsirin ayar da tace a daki a ace a alkur’ani

Tambaya Ɗaya Amsa Ɗaya
Naziru Sarkin Waƙa fa ba cewa ya yi a daki mata ba, ba da’awa ya ke yi akan a daki mata ba. Kuma ko a yadda Ayar ta zo, waɗanne irin mata aka ce a daka ne? Me ya haɗa macen kirki wacce ta ke zaune da miji lafiya da tayar da jijiyar wuyar an ce a daki mata? Kamin dukan me sauran Ayoyin surar su ka ce ayi ne a matsayin ladabtarwa kamin a kai ga dukan? Sannan wane irin duka? Kuma ta wace siga? Ba fa akan ma’ana ko fassarar Aya ake magana ba.

Shi fa Naziru, martani ya ke yi wa wasu mata ne (Ƴan Feminist) da su ka ce babu in da a cikin Alƙur’ani Allah ya ce a daki mata. Shine ya kawo musu Ayar, ya nemi su ma su kawo wacce ta ce kar a daki matan. Shikenan fa!
Ƙaryata Ayar Alƙur’ani su ka yi fa a kaikaice, shi kuma ya kawo Ayar tare da ƙalubalantar su a kan samuwar ta, bayan sun ce babu ita.
Ga bidiyon cikakken bayanin na shi ga duk mai son sanin ainahin abun da ya ke magana a kai don yi wa tambayar ta sa adalci:

https://youtu.be/eaO3q3fZdxM

Daga baya kuma Naziru sarkin waka ya sake kawo wata hujja da tafsirin Sheikh lawal Abubakar triumph inda ya nuna cewa wasu haushina ne suke ji , ba yadda ayar ke nufi ba.
Na fahimci Wasu haushina suke ji, to ga jawabin bada hakuri nan daga Bakin Malam????????…. Allah yasa mu dace!!!”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button