Kannywood

Rai ya bace: An maida mu kaji sai murkushe mu ake yi a Arewa – Gargadin Rahama Sadau ga gwamnatin Buhari

Rai ya bace: An maida mu kaji sai murkushe mu ake yi a Arewa – Gargadin Rahama Sadau ga gwamnatin BuhariFitacciya jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta gargadi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da su shiga taitayin su kada fa kwanto kura, yan Najeriya su fusata.
Sadau ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta ta Instagram inda tace rayukan ‘yan Najeriya ba a bakin komai ya ke ba yanzu kama ga yadda yan bindiga suka mamaye ko ina a yankin Arewa suna kisa yadda suka dama kuma babu abinda ka aiya yi a kai.

A wannan sako wanda ta rubuta a cikin harshen turanci duk da ta saka wasu cikin harshen Hausa, Sadau ta ce Tura fa ta kai bango yanzu.hausa leadership na ruwaito
Irin hotunan da muke gani ana saka wa a shafukan yanar gizo hutunan ne masu tada hankali matuka. Abin tambaya menene talakawan najeriya suka yi da aka bari wadannan mutane na gallaza musu azaba.

” Wai shin laifin mu shine kawai don mun Zabe su. Ina nufin dukkan su da ke kan mulki a kasar nan. Wai yaushe za a sauraremu a kawo mana dauki, a maida hankali wajen kawo karshen kisan gillar da ake yi wa mutane musamman ‘yan Arewa a yanzu. Idan kuka ji sun garzayo sun waiwaye mu to shekarar zabe ya kunnu kai ne.

” Wannan rashin tsaro yana gidan kowa a yankin Arewa, adai yi hattara kada allura ta hako garma. Talaka a yau, zama a cikin gidansa ma tsoro yake bashi.

“Idan kowa ya mutu Sai muga wanda zai zabe su. Zubar da jinin ya isa haka

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button