Labarai

Zamu sake karbo bashin Dala Milyan dari biyu $200m ne domin sayo gidan maganin sauro ga talakawa ‘yan Nageriya ~Cewar Gwamnatin Buhari

Gwamnatin Tarayya tace za’a karbo bashin Dala Milyan dari biyu domin sayen maganin maleria da Kuma Gidan sauro Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, a ranar Litinin din da ta gabata ne ya Bayyana hakan yana cewa kudaden da aka ware dala miliyan 200 za a sayo gidan sauro ne na shirin kawar da zazzabin cizon sauro a jihohi 13.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kan cutar COVID-19 a Abuja.

A cewar Ehanire, ya zama dole a fayyace lamarin saboda jita-jitar da ake ta yadawa game da asusun.

Jaridar PUNCH da Jaridar mikiya na ruwaito cewa, kwamitin majalisar dattawa mai kula da lamunin cikin gida da waje, a yau ranar Talata, ya yi fatali da bukatar da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta yi na karbar bashin dala miliyan 200 a karkashin shirin zazzabin cizon sauro domin siyan gidajen sauro a Cikin kasafin kudin shekarar 2022.

Kwamitin ya yi Allah wadai da wannan bukata da Kuma martani da ma’aikatar lafiya ta mika game da aniyar ta na karbar bashin kudin sayan gidajen sauro ga jihohi 13 masu rauni.

Ehanire ya bayyana cewa, kasar Amurka da asusun kula da lafiya na duniya sun yi alkawarin bayar da tallafi domin kawar da cutar zazzabin cizon sauro a wasu jahohin kasar inda ya kara da cewa asusun ba wai kawai na sayan gidajen sauro bane illa kawar da zazzabin cizon sauro a jihohi 13.

Ya ce, “Hukumar da Shugaban Amurka ya kafa kan cutar zazzabin cizon sauro ta ba da gudummawar dalar Amurka miliyan 295 don tallafawa jihohi goma sha daya da asusun kiwon lafiya na duniya na cutar tarin fuka da zazzabin cizon sauro, ya kuma bayar da kusan dala miliyan hudu ga jihohi 13. Wannan ya bar jihohi goma sha uku ba su da goyon bayan kasashen biyu.

A matsayin sharadi ga abokan huldar mu na sakin nasu tallafin, abokan huldar na son Najeriya ta dauki nauyin jihohi goma sha uku wato Abia, Anambra, Borno, Edo, Ekiti, Ondo, Kogi, Imo, Lagos, Rivers, da kuma babban birnin tarayya. Wannan bashi da zamu karbo ba iya siyan gidajen sauro ba ne kamar yadda ake fayyace zamu siya harda kayan gwaji da sauransu.

Zazzabin cizon sauro na Daya daga Cikin cutattukan da kasahen Africa Suka Saba da ita kamar yadda Bincike ya nuna.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?