Uncategorized

Sumbata Kiss na Karin Tsawon rai ga bil’adama – Binciken masana

Wata marubuciya da masaniyar abincin dake inganta garkuwar jiki dake kasar Amurka Jeena Schreck ta bayyana wasu hanyoyin da Sumba ke inganta lafiyar mutane.
Ga hanyoyin
Sumbata na Kara dankon soyayya a tsakanin masoya
Sumbata musamman tsakanin masoya na cikin hayoyin dake taimaka wa mata wajen amincewa da namiji wajen yin jima’i ko aure.
Faranta rai
Sumbata hanya ce dake faranta wa mutum rai yana kuma taimakawa wajen rage gajiya a jiki.
An ce gamsuwar da ake samu a lokacin da ake sumbartar masoyi kusan dai-dai yake da irin dadin da wanda ke maskewa da Heroin.
Inganta fatar mutum
Musamman ga mata sumbatar masoyi na kara hasken da annuri a fuskar mace ta rika sheki tana
Sumbata na taimaka wa mutane da dama wajen samun gamsuwa kafin jima’i. Sannan yana taimaka wajen inganta sha’awar yin jima’i ga masoyi da masoyiya.
Sumbata na kara tsawon Rayuwa: Wani sakamakon bincike da Arthur Szabo ya gudanar ya nuna cewa sumba na kara tsawon rayuwar mutane a duniya.
Sakamakon binciken ya nuna cewa muddin namiji na sumbar matarsa da safe kafin ya tafi wurin aiki yana kara tsawon rayuwarsa domin zai tafi aiki cikin jin dadi da anashuwa.
Duk da haka akwai wasu hanyoyi da suka nuna cewa sumba na cutar da lafiyar mutane inda haka ya zama dole mutane su rika yin hatara da irin mutanen da suke Sumba.
Cututtuka shida da ake kamuwa da su ta hanyar sumba.
Tarin fuka
Mura da tari.
Kwayoyin ‘Bacteria’ dake kama hakora da saka warin baki.
Hepatitis B
Cututtukan sanyi kamar ‘Herpes’, ‘Gonorrhea’, Syphilis da sauran su.
Cutar ‘Meningococcal’: Cutar na kama da cutar sankarau domin yana kama kwakwalwa da kashin baya sannan ana kamuwa da shi ta hanyar yin Sumba
An wallafa wannan labari a mbg love premium time.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button