Kannywood

Matar Bawa Maikada Na Shirin Kwana casain Rahama Mk Tayi Auri A sirance

Matar Bawa Maikada Na Shirin Kwana casain Rahama Mk Tayi Auri A sirance
Amarya cikin kwaliya inda ta wallafa a shafin na sada zumunta tana godewa Allah

A dai dai lokacin da masu kallon shirin Kwana Casa’in su ke shirin su ga yadda za ta Kaya da Matar Bawa Maikada Rahama M K, Sai ga shi ta yi aure a cikin sirri.
Domin kuwa a safiyar ranar Asabar din nan 6 ga watan Nuwanban da muke ciki ne aka daura auren Jarumar da angonta a gidan su da ke birnin Kano cikin wani yanayi na sirrin da ba kowa ya Sani ba.
Daman dai Jarumar ta Dade tana shirin auren, to sai dai ba ta bayyana ba, Sai kawai aka ji ta yi auren.
Lokacin da wakilin Jaridar Dimokuradiyya ya nemi jin ta bakin ta ta wayar tarho, jarumar ta tabbatar da maganar in da ta ce;
Matar Bawa Maikada Na Shirin Kwana casain Rahama Mk Tayi Auri A sirance
Duk cikin kwaliyar Aure kenan

“Daman kamar yadda na fada maka kwana uku da suka wuce zan yi aure a wannan ranar, Kuma ga shi Allah ya cika mun buri na, Kuma fatan da nake da shi Allah ya sa na samu haihuwa Kuma na mutu a dakin mijina” inji ta
Dangane da fim kuwa, jarumar ta ce, za ta ci gaba da fitowa a cikin Shirin Kwana Casa’in, Sai dai Kuma sauran fina-finai ne “babu tabbas.” A cewar ta

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button