Addini

Ga Dr Sani R. Lemu, akan Hadisin Annabi (SAW) akan iyayen Annabi, ku saurara da kyau

Bayan rubutun jiya naga wasu, sun gagara karyata maganata sun dawo da salon cewa,, “ina son a zagi sauran malaman sunnah kamar yanda ake zagin Dr Jalo.
To gaskiya ban gane ba, shin dan yan bid’a zasu zagi wani malami sai muki yada hadisin annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa sallam? Yo indai hakane ku saka malaman ku su daina karanto Hadisin da yake cewa, “Duk bid’a batace kuma duk bata makomar ta wuta”.
Domin wannan hadisin a kullum yan bid’a suna zagin malaman sunnah akai saboda suna rushe bidi’ar su.
Ga Maulidi ai shi kam kacokan akan Annabi akeyi, meya hanaku tarayya dasu ko ja baki kuyi shiru? Yo ai shi kam babu hadisin daya hana yinsa, amma anyi ittifakin bid’a ne, kuma kowani shekara kuna babatu akai, amma yau ga Hadisi sahihi, yana Muslim da wasu manyan littattafai, kawai dan malamin ku bai fahimta dai dai ba, sai ku hau Youtube kuyi ta rashin kunya da babatu akan Dr Jalo Jalingo? Kunji yan rainin wayo.
Koda yake Dr Sani ya gama magana ya nunar a zancen sa cewa, duk masu babatu yan bid’a ne.
Yanzu ga Video nan ku saurara, na rufe maganar Dr Sani R. Lemu, zamu motsa zuwa ga malami na uku, zamu kawo bayanan sa sannan mu daura muku sautin sa.

Allah ya karawa Dr Jalo Jalingo lafiya da sabati, duk wanda zai baje ya baje, idan akan Hadisan Annabi ne, a duk yanda suka zo, muddin sahihai ne, babu ruwan mu da wanda zaiji haushi ko raba kawuna, duk kawunan da basu hadu akan hadisan annabi ba, Allah kada ya hadasu.
Muhammad Ismail Ali.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button