LabaraiLabaran Aure

Bayan Ta Auri Kanta-Da-Kanta Da Kwana 90 Ta Saki Kanta Bayan Haɗuwa Da Wani Saurayi (hotuna)

Wata budurwa mai tallan kayan sawa mai suna Cris Galera mai shekaru 33, ta saki kanta bayan da ta auri kanta da kwana 90.

Tun a watan Satumba data gabata ne Galera ta bayyana cewar ta auri kanta, kamar yadda ta wallafa hotunanta cikin farin ciki a gaban wata coci sanye da farar riga da fulawa riƙe a hannunta.Bayan Ta Auri Kanta-Da-Kanta Da Kwana 90 Ta Saki Kanta Bayan Haɗuwa Da Wani Saurayi (hotuna) Bayan Ta Auri Kanta-Da-Kanta Da Kwana 90 Ta Saki Kanta Bayan Haɗuwa Da Wani Saurayi (hotuna)

Cris ta bayyana cewar, ta gaji da jiran mijin aure, dalilin da yasa ta kenan yanke hukuncin auren kanta, inda ta rungumi zaman kaɗaici kuma bata jin takaicin rashin mijin.

Sai dai kuma ƙasa da watanni 3 Cris ta bayyana cewar ta saki kanta, sakamakon ta faɗa tarkon soyayya da wani mutum na musamman.Bayan Ta Auri Kanta-Da-Kanta Da Kwana 90 Ta Saki Kanta Bayan Haɗuwa Da Wani Saurayi (hotuna)

A ƙarshe Cris ta bayyana cewar taji daɗin sakin kanta da tayi.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?