Labarai

sakin baki ta Facebook a kan Ganduje ya jawa wani zuwa kurkuku

sakin baki ta Facebook a kan Ganduje ya jawa wani zuwa kurkukuKotun majistret mai lamba 10 karkashin mai shari’a, Muhammad Jibrin, ta aike da wani mutum gidan gyaran hali.

Mutumin mai suna, Sadi Bala Lamido, a na zargin shi da laifin sakin baki a kan gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Freedom radio tana mai cewa Kunshin zargin ya bayyana cewar, Sadi Bala Lamido, ya yi rubutu a dandalin sada zumunta na Facebook, inda ya yi wasu kalamai marasa kan gado, wadanda wasu ke zargin cewa da gwamnan Kano ya ke.

Yayin da a ka karanta masa tuhumar, mutumin Sadi Bala Lamido, ya musanta zargin wanda lauyan da ya ke kare shi ya roki kotun da ta sanya shi a hannun beli.

A nan ne lauyan gwamnati, Barrister Lamido Soron Dinki, ya ce ya na da suka kuma ya roki kotun da ta sanya wata ranar, domin ya yi suka a kan rokon bayar da belin.

wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewa, kotun ta tsayar da ranar 15 ga wannan watan, domin lauya Lamido ya gabatar da suka a kan rokon neman beli.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?