Kannywood

Na daina sanya sabbin jarumai a fina-finai na – Bashir Mai Shadda

Na daina sanya sabbin jarumai a fina-finai na – Bashir Mai Shadda
Bashir Abubakar Mai Shadda

Mashiryin fina-finai a masana’antar Kannywood Abubakar Bashir Mai Shadda ya bayyana cewa ya daina sanyan sabbin jarumai a cikin fina-finansa.

Abubakar Bashir Mai Shadda ya shaida hakan ne a wata hira da Freedom Radio ta yi da shi a ranar Litinin.

“Da yawa daga cikin sabbin jaruman da ake sawa a fina-finai suna shiga harkar ne ba tare da sanin iyayensu ba daga baya kuma su koma fitsararru a idon duniya”.

Mai Shadda ya ce “A ina samun kiran waya fiye da hamsin a wajen ƴan matan da suke so ya sanya su a harkar fim, saboda haka ne ma na ke ba su shawara da cewa su koma makaranta don neman Ilimi in ko hakan ya gagara su nemi miji su yi aure”.

Mai Shadda ya ci gaba da cewa, su kan su ragowar matan jaruman da suka yi fice a masana’antar yana yi musu fatan Allah ya fito musu da mazajen aure domin su samu su raya sunnar ma’aiki.

“Abin yayi yawa a masana’antar, don haka kamata yayi su rika yin sana’o’i ba sa harkar fim ba don haka haƙƙin iyaye ne su sanya ido kan yaran su don hana su faɗawa wasu halaye marasa kyau” in ji Mai Shadda.

Ko da aka tambaye shi me yasa su maza fim ɗin basa auren ƴan matan fim ɗin? sai ya ce “Ai dukkanin mu muna da mata kuma kowa da nasa dalilin na ƙin auren ƴar fim kuma wasun mu suna da mata 4 to babu halin ƙari”.

A wannan lokaci ana samun sabbin jarumai a harkar fim musamman ma a cikin fina-finai masu dogon zango.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?