Addini

Hukuncin Maɗigo Da Illolinsa A Musulunci – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin Maɗigo Da Illolinsa A Musulunci - Sheikh Aminu Ibrahim DaurawaYana daga cikin babbar musifa a wannan zamani, yaɗuwar madigo tsakanin Zawarawa da ƴammata da matan aure,
madigo shine mace ta nemi mace ‘yar uwarta, domin taji dadi da ita, ta gamsar da ita kamar yadda namiji zai gamsar da ita.
Madigo wanda a turance ake kira da lesbianism yana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin mace-da-mace ta amfani da halittarsu, domin kauda sha’awar junan su. Idan wannan ya kasance a tsakanin namiji da namiji to ya koma luwadi kenan. Wal iyazu billah!
Wannan musifa da bala’i na neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut (AS). Wanda tarihi ya nuna cewa shaidan ne yazo a cikin siffar ‘yan Adam, ya nuna wa mutanen Annabi Lut (AS) yadda zasu rinka neman junan su.
A yau, an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar yanar gizo (internet), na daya daga cikin hanyoyin da ke koyar da wadannan munanan dabi’u, musamman a social media, inda zaka tarar a can da suna yi a boye, yanzu kuwa sun fito fili har groups su ke da shi daban-daban a Facebook, WhatsApp da sauran su. Wani abin takaici shine, sai ka tarar har da Musulmai.
Wannan sharrin yahudawa ne, kuma sannu a hankali suna samun nasara a kan mu!
Madigo da luwadi wata mummunar dabi’a ce da ko dabbobi mafi yawa basa neman jinsin su , amma sai gashi ya bayyana ga ‘yan Adam. Allah ya la’anci mai yin sa. Kuma wanda duk Allah ya la’ana to wallahi babu shi babu albarka a rayuwar shi. Kuma babu shi babu samun alkhairin duniya da na lahira har sai ya tuba.
Biyewa sha’awa da son zuciya, da bin bayan dabbobi a surar mutane, har takai, an fara samun auratayya tsakanin jinsi gida mace da mace namiji da namiji, waiyyazu billahi.
Mala’iku suna da hankali amma basu da sha’awa. Mutane suna da sha’awa kuma suna da hankali. Su kuwa mafi yawan dabbobi suna da sha’awa amma basu da hankali. A nan, a duk lokacin da hankalin dan Adam ya rinjayi sha’awarsa to sai ya koma daga cikin mala’iku, domin sune ke da hankali amma basu da sha’awa. Idan kuwa sha’awar Dan Adam ta rinjayi hankalin sa to sai ya koma daga cikin dabbobi, domin sune ke da sha’awa amma basu da hankali.
Madigo da luwadi musiba ce ta shigo cikin al’ummah wadda zata iya haddasa kowane irin fushin Ubangiji. A yau bala’o’in da muke ji suna faruwa a wasu kasashen waje, kamar girgizar kasa, iska da tsawa gami da kashe-kashe da yake-yake da zubar da jini babu kakkautawa, gasu nan biye da mu, ba domin komai ba, sai don wadannan miyagun ayyukka da ke gudana a cikin al’ummar mu.
Ta fannin zamantakewa da kiwon lafiya kuwa, hakika akwai illoli masu yawa da madigo da luwadi ke haifarwa a jiki kamar haka:
1. Su na kawar da sha’awar aure baki daya. Domin a addinance da kuma al’adance akan daura aure ne tsakanin mace da namiji. To macen da take madigo zata kasance bata sha’awar namiji baki daya. Ko tayi auren, tayi ne kawai, amma ba zata yi sha’awar mijin ba.
2. Ba zata sami biyan bukata a kwanciyar aure ba. Shi kuma jima’i a tsakanin ma’aurata, yana kara gina so da kauna a tsakanin juna. Koda an sadu da ita, to ba zata ji sha’awarta ta gushe ba har sai ta hadu da ‘yar uwarta mace sun goga da juna. Shi yasa kake ganin matan aure na aikata wannan mummunar dabi’ar.
3. Madigo na haifar da yaduwar ciwon sanyi.
A duk lokacin da wadda take dauke da ciwon sanyi tayi tarayya da wadda bata da shi, to anan zai yadu. Domin wannan discharge din yana dauke da kwayoyin cuta da zai yadu ya shafe ta.
4. Madigo yana haifar da cututtukan da ke sa kaikayi ga farjin mata. Idan mai kaikayin mara ko kuraje a cikin farji ko zubar farin ruwa, sanadiyyar wani infection, kamar na vulvo vaginal candidiasis, yeast infection, da sauran su, idan suka yi gogayya da juna, to zata dauki wannan ciwon.
5. Madigo yana haifar da yaduwar cutar Kanjamau/Sida (wato AIDS). Kuma ban ga yadda za’a kare wannan kwayar cutar ba, domin takan biyo ruwan dake fitowa a gaban mace ta shafi ‘yar uwarta, kuma ba za’a iya yin amfani da condom ba, kuma ma bincike ya nuna cewa Condom ba ta iya kare komai. Kawai magani shine, aji tsoron Allah a daina (Abstinence).
6. Madigo yana haifar da ciwon mara – Dama, su mata sun fi kowa yawan ciwon mara, wasu ma da shi aka haife su, wasu kuma a lokacin al’ada yake zo masu, wasu kuma daga baya suka dauko shi a wani wuri (infections). Gogayyar da suke yi gaba-da-gaba da juna na haifar da kamuwa da ciwon mara, musamman na infections. Ayi ta faman neman magani a rasa sanin dalili.
7. Madigo yana haifar da ciwon ruhi (spiritual problems) – A nan, shi ciwon ruhi ba fa ciwo bane da zaki gani a zahiri, amma a hakika zaki ji alamunsa a gangar jikin ki. Na farko dai zai busar da zuciyar ki, sai ya kasance baki shakku ko tinanin zaki iya mutuwa a kowane lokaci. Sha’awarki zata gushe ta koma ga ‘yan mata kawai. Da zaran kin ga mace mai girman kirji ko mai manyan duwawu duk sai sha’awarta ta kama ki. Sannan komai nisan ki da ita zaki iya neman ta. Har ki tsufa zaki kasance kina ganin sha’awar mata ‘yan uwanki.
8. Sirrance zai janyo maki gushewar farin jini a fuskar maza, sai kiga duk masoyanki mata ne, gaki kyakkyawa amma ba mai so, basirar ki tabi ta dushe, tunanin ki ya sauya. Wata rana sai ki kasa daina wa. Kuma zuwa gaba sai ya busar da ke, ki rinka ramewa, duk ni’imar jikin ki ta mace, ta gushe, kibi ki bushe, kiyi matukar muni. Kuma a lokacin sai kiyi dana-sani, a lokacin da dana-sanin ba zai amfane ki ba! Allah ya shirye mu baki daya, amin.
Don haka ina kira ga Malamanmu da Masarautunmu da Gwamnatocinmu da likitocinmu da masana hakayyar ‘yan Adam (Psychologists) da Hukumomin kula da harkar fina finai da kuma Matasanmu masu kishi da dukkanin masu ruwa da tsaki wurin ci gaban wannan al’ummah da zaman lafiyar ta, da mu tashi tsaye baki daya, mu hada karfi-da-karfe mu yaki wannan mummunar al’ada ta luwadi da madigo a cikin al’ummah, kafin mu jawo wa kan mu fushin Allah!
In ban da toshewar basirah da kuma kokarin yin fito-na-fito da Allah ba, wai ace namiji ya kwanta da namiji dan uwansa ko kuma mace ta kwanta da mace yar’uwarta!!
Ya zama dole a kan mu, mu tashi muna tallata addinin mu da al’adunmu, bawai turawa ne zasu ringa yi muna tallan al’adunsu ba, balle suyi muna tallar al’ada irin ta luwadi da madigo.
Allah ya halakar da mutanen Annabi Lut, ya kuma nuna wannan mummunar alfasha ce wadda ba wanda ya fara a duniya in ba su ba. da yake bayanin yadda ya halakar da su, ya nuna muna ruwan duwatsu da Allah yayi masu ba babba ba yaro, duk aka halakar da su.
Ina fatan duk masu irin wannan hali Allah ya shiryar muna da su, mu kuma Allah ya kare mu daga irin wannan mafi munin aikin dabbanci, Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button