AddiniFATAWA

Hukuncin Auren Kisan Wuta A Musulunci – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin Aure - Sheikh Aminu Ibrahim DaurawaRashin hak’uri da fushi da rashin sanin Hukuncin aure da saki da gaggawa, ya kan sa mutum ya saki matar sa saki uku, sai kuma daga baya ya ji har yanzu yana son matar sa kuma gashi shari’a ta ce lallai sai ta yi aure, da wani mijin sun yi tariya irin ta aure, sai gama mutum ya shiga damuwa yana tunanin kada ta tafi ta ki dawowa don haka sai ya haɗa baki da wani ya aure ta, da sunan auren kisan wuta. To mainene Hukuncin irin wannan auren.

Dukkan matar da aka mata saki uku ba ya halatta wani ya aure ta da niyyar zai halattata ga mijinta, ko an yi wannan auren bai yi ba. Domin akwai mutanen da ake haɗa baki da su ake yin irin wannan auren. Shi ne bahaushe yake ce masa auren kisan wuta. Sai mutum ya saki matarsa saki uku. Sai kuma abin ya dame shi. Ƙarshe sai ya je ya haɗa baki da wani ya je ya aure ta , sannan ya sake ta don ya samu damar sake dawo da matarsa. Ana yin irin wannan wani lokacin ma hatta waliyyan miji da mata da su ake ƙulla hakan. Wani lokacin kuwa tsakanin miji ne da matar da ya saki.
Saboda gudun irin wannan ne musulunci ya ja hankalin mu da cewa mu dinga yin lissafi da mu daina gaggawa musamman cikin lamarin sakin aure.
Ma’aurata da yawa suna samun kansu a irin wannan hali. Su ƙi haƙuri su kashe aurensu , ƙarshe kuma a dinga nadama ana tunanin makomar yara da sauransu..

Mu na yawan samun tambayoyi akan irin wannan daga ko ina.
Akwai wani da ya yi min waya daga wata jiha yana tambaya akan cewa ya saki matarsa amma yanzu kuma ya shiga damuwa. Kullum kuka yake yi ita ma matar kuka take yi. To sai ya samu wani abokinsa ya ce ya taimaka masa zai ba shi kuɗi. Ya ce ya je ya nemi auren ta daga an ɗaura aure ta tare a gidansa sun sadu sai ya sako ta, shi kuma sai ya mayar da ita.
Sai Na ce to masa “ai wannan auren bai yi ba.
Shi nasan in ya yi shi da wannan niyyar bai yi ba. Kaima nakan da za ka yi a bayansa bai yi ba. Ka ga duka biyun babu wanda ya yi. Saboda haka tunda har ka keta shari’a, ka yi abin da ba’a sa ka ba, sai a yi haƙuri har sai ta samu wani mijin da kanta.”
Haka nan kuma ita matar ita ma ba za ta kirawo wani ta ce zo ka aure ni zuwa lokaci kaza ka sakeni ba. Ita ma idan ta yi haka auren bai yi ba.

Domin abin da ake gudu yin auren da mutuwarsa an sa masa lokaci, kuma an sa masa sharaɗin da shri’a ba ta yarda da shi ba. Amma idan wani ne kawai tausayi ya kama shi a ransa ya je ya aure ta don ya gyara tsakaninsu ba tare da miji da matar sun sani ba , to wasu malaman na ganin auren ya yi. Duk da cewa babu kamala da mutuntaka a cikin yin hakan. Domin duk sanda ya sako ta , to sai an dinga zargin cewa daman auren kisan wuta aka yi, musamman idan da sanayya. Kuma ta iya yiwuwa ita matar tsakani da Allah ta aure shi kuma ta fi samun nutsuwa a gidansa amma ya sake ta. Ƙarshe ya zamo ta yi biyu babu. Ta rabu da shi ita kuma ba zata iya komawa gidan tsohon mijinta ba.
Irin wannan auren wasu malaman suna sanya shi a babin ” An Nikahu Bi Niyyatid Ɗalaƙi ” wato mutum ya yi aure da niyyar zai saki matar. Wanda akwai sananniyar magana da saɓani akansa.

A wani lokacin kumai ita matar ce take ƙudurcewa a ranta cewa za ta yi aure, amma mijin da za ta aura dama ba wani miji na a zo a gani za ta samu ba. Tana son ta samu dai gara-gara haka. Kawai ta je ta same shi ta lallaɓa shi ta aure shi da zarar sun sadu a daddafe shike nan sai ta bijire masa. Idan ta bijire masa tai ta ɓata masa rai, taƙi yarda da shi har sai ya gaji ya sake ta.

Wasu ma har maganin hana ɗaukar ciki suke sha, gudun kada ciki ya samu a wannan saduwar.Burin ta dai kawai ya sake ta bayan ya sadu da ita.
Idan ya sake tan sai ta zo ta yi idda ta koma gidan mijinta na da. Duk wannan ma malamai suna ganin auren ya yi amma fa ba ta dai kyautawa wanda ta aura ba. Domin akwai sakamako na yaudara da cin amana da ɓatawa miji da yake jiranta. Sannan zai wahala mace ta yi irin wanna kuma ta samu abin da take buri , domin Allah ba ya datar da mutane masu yaudara da cin amana.

A taƙaice dai auren kisan wuta yana da mataki guda huɗu. Biyu daga cikin sun haramta kuma aure bai yi idan aka yi su Biyu daga ciki biyu kuma sun halatta, amma a kwai rashin mutuntaka da ƙima da daraja a cikinsu
Biyun da suka haramta su ne, mjin ya sa wani ya je ya aure ta dan ya dawo da ita. Ko kuma ita matar ta umarci wani ya aure ta don ya saketa ta koma.Wannan biyun ba su halatta ba.
Waɗanda suka halatta aure su ne, ita matar ta ƙudure a ranta cewa za ta yi aure ne na kisan wuta don ta koma gidan mijinta amma shi wanda aka yi auren bai san da wannan ba Ita kaɗai ta shira kayanta a zuci kuma ta yaudari wani ta lallaɓa ta aure shi.

Ƙarshe kuma tai ta gasa masa aya a hannu har sai ya sake ta. Duk wani yanayi na tsabta , kwalliya girki , magana mai daɗi ba zai gani a tare da ita ba.Wata ma ta gwammace ta yi Khul’i ta biya shi sadakintsa,; kamar yadda wata mata ta zo, gurin Manzon Allah (SAW) ƙarar mijinta . Sai ya ce kina son ki koma gidan tsohon mijin ki ne ?
Saboda haka ki mayar wa da wannan abin da kika karɓa a hanunsa na gonarsa. Ka ga manzo Allah (SAW) ya gano cewa akwai soyayyar tsohon mijinta a ranta kuma nan take so ta koma. Amma bai hanata ba, tunda ba za ta iya zama da wannan ba tunda ga abin da ta sa a ranta.

Na biyun kuma shi ne wanda wani zai zo bisa ratsin kansa ya auri mace don ya sake ta , ta samu damar komawa gidan tsohon mijinta ba tare da sanin kowa ba. Shi ma wannan mun magana a kansa cewa babu mutuntaka a ciki duk ya halattawa ɗaya mijin aurarta..
Allah ya sa mu dace.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?