Labarai

Hattara Iyayen Matan Arewa :Yadda Cutar Madigo Ta Haifarwa wata Budurwa cutar’ Cancer of Vagina’

Hattara Iyayen Matan Arewa :Yadda Cutar Madigo Ta Haifarwa wata Budurwa cutar' Cancer of Vagina'Iyayen Mata Musamman na katsina kuyi hattara (da muguwar ‘dabiyar Madigo) da ta tunkaro ‘ya’yan ku (‘yan mata).
Wata medical Doctor ta Bukaci in Isarda wannan Sako duk yanda zan iya domin yakar wannan Musiba (ta madigo). Gayanda tattaunawarmu ta kasance a waya.
Bayan Mun gaisa, ta yi min bayanin kanta da kuma ma’aikata (ko Assibitin da take) Sai take Cemin.
“A binda ke faruwa yanzu a Arewa musamman anan katsina shine zaka samu wata macce da basu hada komai da yarinya ba tana yi mata hidima tana Madigo da ita.”
Na ‘danyi Shiru, Cen Sai Nace “Subhanallahi.” Sai taci gaba da cewa,
“Wato wata yarinya ce ta kamu da Cancer Of vagina tun abin yana Infection har yakai Cancer wanda ina ganin ba’a nigeria ba ko a turai zaiyi wuya a samu maganinsa”
Nace “Subhanallillahi, Ya Salam!.”
Taci gaba da Cewa, “Yanzu Kusan Shekara ‘daya kenan Wannan yarinyar na zuwa waje na Domin karbar Tretment na Infection, amma abinda yake bani mamaki kullum shine, sai taji Sauqi sai kuma abin ya dawo, to a haka dai har yanzu ta kamu da Cancer of Vagina.”
Taci gaba da gayamin, “Lokacin da naga wayannan kuraje da Ruw masu warin sun fesowa wannan yarinyar, Sai nake tambayarta, ko menene dalilin wannan matsala kuwa, Me take anfani dashi haka?”
“Shine take gaya min Wallahi ba komai take amfani da shi ba, Sai dai madigo da wata mata ta sanya ta, ta hanyar yi mata hidima.”
(Wa’iyazubillahi), Wannan Likita ta shaidamin da suka yi bincike da kyau sai suka gano ai abin ya yawaita.
Yarinya bata hada komai da Macce ba sai ta rika yi mata Hidima, kudin kashewa, dinkin Sawa, kayan Shafe-shafe da wasu abubuwa na yau da kullum.
Shine ta roke ni akan yi sanar a duk yanda zan iya sanarwa matsalar da Matan Katsina Suke ciki.
Babu Shakka Wannan Abu ba karamin Bala’I bane, Sannan Ba karamar musiba bace ke tun karo mu ‘yan Arewa.
Babu shakka Yana da matukar Kyau Iyaye su san Dawa ‘ya’yansu suke Qawance, Sannan Idan Sun fita Ina Zasu je.
Sannan Suma ‘ya’yan Yana da matukar muhimmanci su dogara da Allah Wallah Idan Allah ya Kaddare ka da Arziki ko mai tsiya sai kayi shi.
‘Yan Matan Arewa Musamman Na Katsina kuji tsoron Allah Kada wajen Neman Duniya Ku rasa lafiyar ku.
Yanzu wannan da ta kamu da Cancer Of Vagina Wannan Likitan ta Shaidamin cewa, duka wayanda suke wannan muguwar mu’amula sun kyaleta, basa kula ta. Idan ma ta kira su basa dauka.
Wallahi duk wacce bata Ji tsoron Allah ta daina Ba, Ita ma hakan Zai faru a gareta. Don haka sai a kiyaye.
Hausawa SunCe, Idan Kunne Yaji Jiki ya Tsira to muddin Ba’ayi aiki da abinda ya jiba to jiki bai tsira ba.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 18/10/2021

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button