Labarai

Gaskia Labari :Yar damfara Ta kashe kanta Bayan Da Ta damfarar wani bawan Allah

Ke duniya ina zaki da mu, rayuwa ta lalace ko ina, a kafar sadarwa damfara a zahiri damfara, wannan ita ce aisha Muhammad nasara, wacce labarin mutuwan ta ya karade social media daga shekaran jiya zuwa jiya, inda mutane sukai ta tausaya mata, su na mata addu’o’i na samun rahma da gafaran Allah, ina daya daga cikin masu mata fatan dacewa da kyakyawan masauki.

Aisha dai ita da kanta ta sanar da cewa zata mutu sabida za’a mata tiyata, amma awani asibiti akai tiyatar, da yaushe akai tiyatar? Duk wannan wani abu ne da ita kadai ta san shi, bal ma ana zargin da da ta taba kashe kanta a wani account din ma mai suna fatima aliyu, a wannan sahar ta Facebook, shima bayan yunkurin damfara ne da asiri ya kusa tonuwa,

Gaskia Labari :Yar damfara Ta kashe kanta Bayan Da Ta damfarar wani bawan Allah
Asalin sunan mai wannan hoto itace Fatima Aliyu wanda Ayshert Muhammad Nasara na karya
Gaskia Labari :Yar damfara Ta kashe kanta Bayan Da Ta damfarar wani bawan Allah
Rubutun mutuwar karya da tayi

Mai yafaru bayan nan? Kwatsam jiya da yamma sai naga wani posting wacce wata tayi sharing cewa wannan yafinyar fa karya take yi bata mutum ba, hasali ma account ne na bogi kuma an bindi diddigin gidan su a gumel dake jihar jigawa babu wata aisha, kuma babu wani wanda ya santa da yace dagaske ta mutu.

Sai na shiga bincike inda na samu number din-ta, inna kira babban mace ke dagawa dana gaishe ta, sai ta bawa namiji wayar, da na ce masa dan Allah na kira ne na mika sakon ta’aziyyar aisha, kawai sai ya kashe wayar, da na kara kira still akai rejecting, sai bayan kamar 5 minute na kira da wata number still aka daga dana ambaci aisha sai aka kashe, abun mamaki da daure kai, nace Allah swtya kyauta nayi gaba.

Gaskiyar magana bisa rubuce-rubuce da al-umma sukai tayi shi ne babu wata aisha da akama aiki, hasali wani ta damfara gudun kar a kamata shi ne ta kashe kanta, bil hakika aisha garjejen gardi ne kawai dan damfara a wannan sahar wanda a baya yayi amfani da account mai suna fatima aliyu shima da aka gano shi ya kashe kan shi.

Ga hotunan screensho nan har daga gidan su mai nasara cewa karya ne basu da aisha, ga kuma wanda suka damfara yayan ta nan tayi magana.

Dole sai munyi da gaske a wannan sahar yan damfara sunyi yawa kuma mu daina ruduwa da kyan mace ko hotan da ta dora, dan wlh yawancin su gardawa ne wasu kuma matan ne, amma b fuskar da suka daura ba ne, yan damfara sunyi yawa.

Manzu dai aisha ta kashe kanta bayan tayi damfara, mu kam sai dai muce suje koma waye Allah swtya shirye shi ko ya shirye ta.

Daga: Usman Rabiu Kwankwaso

Ku kasance da hausaloaded a koda yaushe zamu kawo muku yadda wannan bayin Allah yaudara.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?