Labarai

Da Mawaka da ‘Yan zaman Banza duk daya suke -inji Galadima

Da Mawaka da ‘Yan zaman Banza duk daya suke -inji GaladimaShugaban Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba Alhaji Shu’aibu Umar Galadima ya kira ga Mawaƙa da sukama sana’a domin a cewar sa da mawaƙi da ɗan zaman banza duk ɗaya suke.

Kamar yadda barewaradio na ruwaito Shugaban ƙaramar hukumar Shu’aibu Galadima ya bayyana hakane a lokacin da ƙungiyar mawaƙan ƙaramar hukumar Yamaltu Deba suka kai masa zayarar ban girma a ofishin sa dake Deba fadar ƙaramar hukumar Yamaltu Deba dake jahar Gombe.

Galadima ya ƙara da cewa “Waƙa ba sana’a nace kuma ni a matsayina na ɗan siyasa waƙa bata isa tasa naci mulki ba ko na faɗi saboda haka ina mai baku shawara kutashi kukama sana’a a matsayin ku na matasa” Inji shi.

To sai dai wannan jawabi baiyima ‘yan ƙungiyar daɗi ba kamar yadda ma taimakin Shugaban ƙungiyar Nazeer Ajiyan waka yace ” wannan abu gaskiya bamuji ɗadiba ko bakomai mun kawo masa ziyara ya kamata ace yayi godiya da wannan girma mawan amma kuma baiyi haka sai yayi ta Zagin sana’ar waƙa tare da kusheta”

“Kuma ko yanaso ko bayaso mawaƙa na bayarda cikakkiyar gudummawa wajen cigaban Al’ummar Duniya musamman ma ga ‘yan siyasa” Inji Nazeer Ajiyan waka

Daga karshe Nezeer yayi kira ga’yan uwansa mawaƙa dasuyi watsi da wannan batun sannan susa gaskiya da tsoron Allah acikin sana’ar su ta waka domin a cewar sa Kowace sana’a akwai wuta kuma Akwai Aljanna.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?