Kannywood

Ƙaunar da nake yi wa Annabi Muhammadu ce ta sa na rera waƙar yabonsa- Jaruma Sarah Aloysius

Ƙaunar da nake yi wa Annabi Muhammadu ce ta sa na rera waƙar yabonsa- Jaruma Sarah Aloysius
Stephanie

Fitacciyar jarumar fina -finai a cikin shirin DadinKowa na gidan talabijin na Arewa24, Sarah Aloysius, ta ce matuƙar girmamawar da take yi wa Annabin Musulunci, Muhammad (S. A. W) ne ta sa aka ganta tana rera wakokin yabonsa cikin harshen Larabci a wani faifan bidiyo a shafukanta na Sada Zumunta.

Jarumar wadda mabiyiya addinin kiristanci ce, wacce aka fi sani da Stephanie, ita ma ta bi sahun miliyoyin al’ummar musulmai a sassan duniya domin gudanar da bikin Maulidin Annabi duk da asalin addinin ta.

Da take zantawa da Jaridar Sahelian Times , yayinda hausadaily times na ruwaito cewa Sarah ta bayyana cewa tana da tarin wasu waƙoƙin Larabci na yabon Annabin Musulmai, Muhammadu Rasulullahi (S. A. W).

Ta ce tana sauraron wakokin ko dai a gida ko yayin da take tuƙi.

“Na fara jin waƙar daga wani abokin aikina kuma nan da nan na ji ta kwanta min. Na roƙeshi ya tura miin, nan kuwa na ci gaba da saurara har saida na iya rerawa, ”in ji ta.

Aloysius, ta ce, bidiyon ya ja hankalin jama’a wasu na zagi wasu kuma na nuna  goyon baya.

“A matsayina na Kirista, na yi imani zan iya zuwa coci in rera waƙoƙi yabo kamar yadda nake yabon Yesu, saboda girmamawar da nake yi masa, amma da yawa suna bayyana abin da na yi kamar na wanda ke neman suna a kafafen sada zumunta,” in ji ta. fita.

Lokacin da aka tambaye ta ko abin da ta aikata hanya ce ta karban Musulunci a matsayin addini, sai ta ce “Wadanda ke yi min fatan alheri, su ci gaba da yi min addu’ar fatan alheri, domin Allah ne kadai ya san abin da ya fi dacewa da rayuwar mu,” ta amsa.

“Na girma a Maiduguri, kuma a lokacin da na girma na yi hulɗa da mutane daga addinai daban -daban, kuma an koya mini in girmama addinan mutane.

“Har yanzu muna iya kasancewa da addinai daban -daban kuma har yanzu muna zaune tare da juna cikin aminci da jituwa,” in ji ta.

Musulmin duniya na murnar zagayowar ranar haihuwar annabin musulunci, a duk wata na uku na kalandar musulunci, Rabiul Awwal.
One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?