Kannywood
Na Kwashe Shekarata 36 A Harkar Fim – Cewar Jaruma Hajara Usman
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.


A wannan kashi na 67, shirin ya tattauna da Hajara Usman fitacciya a fina-finan Hausa na Kannywood.
A wannan shiri ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta.
Ɗaukar bidiyo: Abdussalam Usman
Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai
Gabatarwa: Buhari Fagge
Ni Yar Asalin Jihar Gombe Ce, Amma A Lagos Na Tashi. Zuwa Yanzu Na Dauki Shekaru Akalla Talatin Da Shidda Ina Fito Wa A Cikin Fina-finan.
Mafi Yawancin Jaruman Masana’antar Fina-finai Maza Da Mata Na Taɓa Fitowa A Matsayin Mahaifiyarsu A Cikin Fim. Na Taɓa Aure Har Sau Biyu, Ina Da Yara Ukku.
Ga hirar nan ku saurara.