Kannywood

Na hadu da Matsaloli sosai a harkar fim, cewar Jaruma Masa’uda Yar Agadaz

Na hadu da Matsaloli sosai a harkar fim, cewar Jaruma Masa’uda Yar Agadaz
Masa’uda Yar Agadaz

Fitacciyar jaruma a Masana’antar fina-finai ta Kannywood Masauda Ibrahim wacce aka fina da Yar’agadaz ,wacce kuma ta yi suna a cikin shirin Dadin Kowa wato Zuby, ta bayyana irin wahalar da ta sha a harkar fim kafin ta samu ta zama fitacciyar jaruma.

Masa’uda’ Yar’agadaz ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawarta da wakilin Jaridar Dimokuradiyya, inda ta fara da cewar

“To gaskiya na sha wahala, kuma na hadu da Kalubale da dama a cikin harkar fim musamman ma dai sai ka ga wani ya nuna yana son ka a fili, sai ka tafi kuma ya zage ka, to irin wannan na fuskance su da dama, sai dai ina yi musu fatan alheri, saboda yanzu komai ya wuce a waje na, domin idan na ce zan tsaya na lissafa to abubuwan suna da yawa. ”

Na hadu da Matsaloli sosai a harkar fim, cewar Jaruma Masa’uda Yar Agadaz
Masa’uda Yar Agadaz

Dangane da maganar aure kuwa da muka tambaye ta cewa ta yi:

“Ni dai a gare ni zabin Allah na ke nema, duk wanda Allah ya zaba miun shi zan aura, don haka duk masu yi mana kallon muna da buri, to mu ba haka mu ke ba, domin arziki na Allah ne, don haka ba sai lallai mai kudi zan aura ba, miji nagari kawai na ke fatan samu. ” a cewar ta.

yanzu dai suma yan kasar nijar sun cire tuta wajen zuwa nigeria su haskaka a harka fim wanda wannan ya samu asali fegen mata irin yadda fati niger nayi fice a waje rubuta wakoki da kuma rerawa wanda sunka sanya yan kasar kishin suma su zo a dama da su inda a gefen maza akwai su suleman hamma bosho gefen barkwanci da kuma Auta mg boy gefen mawaka wanda shima yana tashi sosai yanzu a fagen wakokin soyayya wansa shine yayi wakar baba ayi mini aure.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?