KannywoodUncategorized

Don Fadarkwa Muke Harka Fim – Rukayya Dawayya

A dai-dai lokacin da a ke yi wa yan fim kallon samu bata tarbiyyar Jama’a, fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, wacce a kasan ita kadai ce ta rage a cikin tsofaffin jarumai da a ke dama wa da ita haryanzu.

Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya. Ta yi kira ga Jama’a da su rinka yi wa yan fim kallo ya’yan da iyayen su ka yi aure suka haife su iyaye su, kuma suka ba su tarbiyya suka saka su a makaranta. ”

Jarumar ta bayyana hakan ne ga wakilin jaridar Dimukaradiyya a lokacin tattaunawar su da ita.

Ta Kara da cewar” Duk abin da aka ga muna yi, ba muna yi ba ne don mu bata tarbiyyar wani, don haka muna kokarin fadakar da Jama’a ne, domin su fahimci yadda rayuwar duniya take. ”

Ta ci gaba da cewa” Ni dai na dauki fim a matsayin harkar Sana’a kamar yadda kowacce mace za ta fito ta tafi aikin Office ko kasuwancin ta, to haka mu ma mu ke daukar fim.” Inji ta.

“Don haka duk in da aka gan mu aiki mu ke yi, kamar sauran mata da su ke yin aiki. Mu kan sa a ran mu mun tafi aikin mu na neman Halak ne, don haka sai a rinka yi mana addu’a a rinka yi mana kallo na adalci. ” a cewar ta.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?