Daga ƙarshe dai an katse Layukan Sadarwa a jihar Katsina
Daga ƙarshe dai an katse Layukan Sadarwa a wasu sassan jihar Katsina
Ƙananan Hukumomin da Lamarin ya shafa sun haɗa da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi waɗanda duk suke makwabtaka da dajin Ruggu Wanda ya kasance maboyar Ƴan Ta’adar Daji a faɗin jihar Katsina.
Sauran yankunan da Lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua, Bakori da kuma Malumfashi.
Daily trust Idan dai ba’a manta ba a cikin Ƴan ƙwanakin nan ne akayi ta yaɗa wata Takardar da ta Ayyana cewa an ɗauke service na layukan Jama’a a faɗin jihar Katsina, Sanarwar da Hukumar da take kula da Kampanonin Sadarwa ta ƙasa ta musanta, Inda ta ayyana cewa Sanarwar ta jihar Zamfara ce ba ta jihar Katsina ba a wancen lokacin.
✍ Muhammad Aminu Kabir