Kannywood

Babban alherin da na samu a Kannywood shi ne aure na da Maryam A. Baba (Sangandale) – mawaƙi Abdul Kafinol

Babban alherin da na samu a Kannywood shi ne aure na da Maryam Sangandale – mawaƙi Abdul Kafinol
Abdul Kafinol tare da maiɗakin sa, fitacciyar mawaƙiya Maryam A. Baba (Sangandale) su na yi wa juna kallon ƙuda

ABDUL Kafinol ya na ɗaya daga cikin matasan mawaƙa kuma jaruman Kannywood masu tasowa. A hankali, a hankali tauraruwar sa na ta ƙara haske a masana’antar.

Sai dai an ɗauki tsawon lokaci ba kowane mai kallo ba ne ya san Abdul ba. Ko a lokacin da ya auri fitacciyar mawaƙiyar nan, Hajiya Maryam A. Baba (Sangandale), wanda hakan ya sa shi ma ya shiga sahun mazan Kannywood da su ka auri ‘yar fim, akwai masu tambayar mecece sana’ar sa? A wane gari ya ke? Hasali ma dai daga lokacin ne wasu su ka fara sanya ido a kan shi.

Mujallar Fim ta samu damar zantawa da wannan matashi mai sauƙin kai tare da girmama abokan sana’ar sa. A hirar, Abdul ya faɗa mana tarihin rayuwar sa da yadda aka yi ya fara waƙa, da ƙalubale da nasarorin da ya samu, da yadda aka yi ya haɗu da Maryam har su ka yi aure kuma su na zaune lafiya tsawon shekara biyu. Ya kuma amsa tambaya kan batun samun haihuwa tsakanin sa da matar tasa. Bugu da ƙari, ya bada shawara ga ‘yan fim masu muradin auren junan su, har ma ga waɗanda ba ‘yan fim ba. Ku karanta ku ji:

FIM: wanene Abdul Kafinol?

ABDUL KAFINOL: To, assalamu alaikum. Da farko dai suna na Abdulrasheed Muhammad, wanda aka fi sani da Abdul Kafinol.

An haife ni a unguwar Goron Dutse. Na yi makarantar firamare a ‘Yan’awaki da ke unguwar Ƙoƙi, sannan na yi ƙaramar sakandire a makarantar Aminu Kano Way, wanda daga baya na tafi makarantar kwana ta gwamnati da ke Ƙaramar Hukumar Ƙaraye, wato Unity School, Ƙaraye kenan, wanda daga baya na dawo cikin garin Kano na ƙarasa a makarantar sakandiren Rumfa.  To daga nan kuma na tafi makarantar koyar da aikin shari’a da malamta, wato ‘Legal’ ta Aminu Kano, inda na yi difloma kan yaren Hausa da Ingilishi. Bayan da na kammala na ƙara ɗorawa a kan wannan karatun da na ke har ta kai ga na samu shaidar malamta ta NCE a makarantar ta Legal. Yanzu dai na kammala, mu na jiran abin da Allah zai yi.

FIM: Ka na ɗaya daga cikin matasan mawaƙa da tauraruwar su ta ke haskawa. Ya aka yi ka shiga wannan fage na waƙa?

ABDUL KAFINOL: E to, harka dai ta waƙa zan iya cewa ra’ayi ne wanda wani lokacin za ka ga magabatan mawaƙa ake samu ko ka ke sauraron su, za ka ga abin ya na ɗan shigar ma jiki har ka yi tunanin ya za a yi kai ma ka shiga sahun su. To a zahirin gaskiya jin ‘yan waƙe-waƙen Hausa shi ne ya sa na ji sha’awar cewa ni ma bari na shigo don bada tawa gudunmawar ko Allah zai sa a saurare ni kamar yadda ake sauraren sauran mawaƙa.

Abdul a bakin aiki
Abdul a bakin aiki

FIM: Sau da dama mawaƙa na fuskantar ƙalubale wajen iyaye a duk lokacin da mutum ya bayyana  ƙudirin sa na zai fara waƙa. Shin ko kai ma ka samu wannan tasgaron daga wajen iyaye?

ABDUL KAFINOL: A zahirin gaskiya ni ban samu wata matsala daga gida ba, tunda kusan waƙar ma daga gida na faro ta inda na fara waƙar biki da na yi wa ‘yan gidan mu. Ni na fara yi musu waƙar biki, to ka ga babu zancen tasgaro daga gida kenan. Gaskiya da nasara na fara daga gida, da kuma ita zan ƙare.

FIM: Bayan wannan shinge da ka tsallake na rashin samun ƙalubale daga gida, ko ya ka tsinci kan ka a industiri, musamman da ka zo a matsayin sabon mawaƙi?

ABDUL KAFINOL: Kawai dai ƙalubale na a industiri shi ne bai wuce yanayin zamantakewa ta in ba ka isa ba ko ba ka kai ba to harkar ba a yi da kai.  Kawai dai harkar industiri ta na amfani da cewa sai ka kai sannan za a yi da kai. To akwai buƙatar sai ka maida hankali a yayin da ka ke so ka gabatar da abin da za ka gabatar, ka toshe kunnen ka, ka kuma rufe idon ka kan duk abin da za ka ji ko gani. Idan Allah ya yi da nasara kuma ka na da rabo sai ka ga an zo dole ma sai an yi da kai. To haka harkar industiri ta ke.

Karanta kuma  Ba na neman kujerar Afakallah duk da yake ya kashe Kannywood – Salisu Officer

FIM: Tun bayan fara waƙoƙin ka zuwa yanzu shekaru nawa ka kwashe a cikin industiri?

ABDUL KAFINOL: Kai, tab! Gaskiya yanzu kusan zan yi shekara bakwai ko takwas.

FIM: A cikin waɗannan shekaru, waƙoƙi nawa ka yi?

ABDUL KAFINOL: A zahirin gaskiya ba zan ce ga adadin waƙoƙi na ba ko kuma nawa ba ne tunda ba ƙirgawa na ke ba, tunda dai lokacin da na buɗe situdiyo na kawai ina yin waƙa ne ni kaɗai. Idan na yi kaya na, kawai zan tura a waya ne, na ci gaba da harkoki na; ban damu da ma sai wani ya ji ba, sai dai ‘yan kusa da ni idan wasu sun saurara su ka nuna su na da buƙata sai na tura musu saboda ba na damuwa da wai sai an ji waƙa ta, ballantana ma na ƙididdige nawa ne su ka fita kuma nawa ne a ƙasa.

FIM: A cikin waƙoƙin ka, wacce ce bakandamiyar ka?

ABDUL KAFINOL: E to, gaskiya bakandamiya ta kuma wacce mutane su ka fahimci cewa ina harkar waƙa saboda a zahirin gaskiya mutane da yawa ba su san ma ina waƙa ba sai sanadiyyar wannan waƙa tawa ta ‘Bakan Gizo’ wadda ita ce ta farko da na fara yi duniya ta san ni, kuma alhamdu lillahi ta fito, Allah ya sa mata albarka, mutane su ka karɓe ta. To kusan ‘Bakan Gizo’ ita ce bakandamiya ta kuma ita ta haska ni a duniya waɗanda ma ba su san ina waƙa ba sai ta dalilin wannan waƙar su ka sani.

Abdul Kafinol a gida
Abdul Kafinol a gida

FIM: Da man wannan waƙar taka ta ‘Bakan Gizo’ mallakin ka ce ba haɗin gwiwa ku ka yi da wasu mawaƙa ba?

ABDUL KAFINOL: To, waƙar ‘Bakan Gizo’ gaskiya ni na ƙirƙiri waƙa ta. Tun da farko ma ni zan rera waƙa ta da kai na, sai na ga ina buƙatar na ɗan sa mata wasu zantuka. To sai na duba cewa su waye na ke da kusanci da su waɗanda za su ba ni gudunmawa a wannan harka, sai na yi tunanin na kira Isah Ayagi, na kira Hamisu Breaker, mu ka haɗu mu ka ɗora wannan waƙar ta ‘Bakan Gizo’. Wannan shi ne abin da ya faru.

FIM: Ko an samu wata nasara bayan fitar wannan waƙa ta ‘Bakan Gizo’?

ABDUL KAFINOL: E, kamar yadda na gaya ma, waɗanda ba su san ina waƙa ba ta dalilin ta sun san ina waƙa. To duk wani abu da na samu yanzu gaskiya sanadin waƙar ‘Bakan Gizo’ ne.

FIM: Ka taɓa fitar da kundin waƙoƙin ka, wato album?

ABDUL KAFINOL: E, na fitar da album, kamar yadda na faɗa mai suna ‘Bakan Gizo’. Iya shi kaɗai na fitar a shekarar da ta gabata.

FIM: Waƙoƙi nawa ya ƙunsa?

ABDUL KAFINOL: Ya ƙunshi kimanin waƙoƙi goma sha shida.

FIM: Bayan sana’ar waƙa, ka na wani abu ne?

ABDUL KAFINOL: Kai, sosai ma! Ina yin sana’ar fentin gidaje da yin kwalliyar gidaje, wato ‘decoration’ a turance, da sauran su. Kuma ka san dole sai an haɗa da wata sana’ar a gefe.

FIM: Na san dai Abdul Kafinol ya na da ɗimbin masoya. Shin idan kun haɗu da masoyan ka wacce tambaya ka fi amsa musu?

Karanta kuma  Abin da kundin waƙoƙin ‘Lokaci’ zai zo da shi – Adamu Nagudu

ABDUL KAFINOL: Abin da masoya na su ka fiya tambaya ta yanzu shi ne a kan waƙar ‘Bakan Gizo’. Su kan ɗan ɗauko wasu baituka wanda za su ce min ko me na ke nufi kamar yadda a waƙar na ke cewa “mai dundumi”, don akwai wanda su ke tambaya ta wai shin menene wannan abu? To a zahirin gaskiya dundumi wani suna ne wanda ba a amfani da shi ko in ce ba kowa ne ya san shi ba. Don yanzu idan za ka tara yara ɗari ba su san menene dundumi ba. To dundumi kuma wanda ya san shi wani ciwo ne da ake yi a ido wanda ga idon dai guru-guru, amma da rana za ka ga mutum ba ya gani sosai. To wanda ba ya gani sosai da rana ka ga in dare ya yi ba abin da zai gani. To wannan shi ne abin da na ke nufi.

Fostar album ɗin ‘Bakan Gizo’ da hoton Abdul Kafinol tare da abokan sa, fitattun mawaƙan nan Isah Ayagi da Hamisu Breaker
Fostar album ɗin ‘Bakan Gizo’ da hoton Abdul Kafinol tare da abokan sa, fitattun mawaƙan nan Isah Ayagi da Hamisu Breaker

FIM: Wane ƙalubale ka samu tun bayan shigowar ka wannan masan’anta?

ABDUL KAFINOL: Ai babban ƙalubale a wannan masana’anta shi ne kawai wa ka sani wa ya san ka. Idan ka na da shi za a yi da kai, idan ba ka da shi to a zahirin gaskiya za a ɗauke ka a wulaƙance kuma a nuna ma ba a ma san ka ba ballantana a yi da kai. Wannan shi ne abin da industiri ta ke ciki.

FIM: Shin akwai wani abu na nasara da ka samu a cikin industiri wanda ba za ka iya mantawa da shi ba?

ABDUL KAFINOL: Abin da ba zan taɓa mantawa ba a rayuwa a harkar industiri ko in ce a harkar waƙa shi ne sanadin haɗuwa da mata ta. Ina ga ba wani abu da zan samu wanda zai wuce wannan na alheri, gaskiya. Duk wani abu da zai zo a bayan samun mata ya ke. To wannan shi ne nasara ta farko da na fara samu a wannan sana’ar.

FIM: Ka na ɗaya daga cikin ‘yan fim da suka auri ‘yar wannan masana’anta. Shin ko ya aka yi aka haihu a ragaya?

ABDUL KAFINOL: E to, gaskiya Hajiya Maryam A. Baba ko in ce Sangandale, na san ta ne a harkar waƙa wanda tun can da ina ɗan jin ta ne a nesa-nesa tun kafin na yi zurfi ma a harkar waƙa, kuma ina ɗan ƙara wayewa ina ƙara matsowa sai na yi ƙoƙarin ya za a yi ita ma na sa ta a jadawalin waɗanda mu ke waƙa tare. Na neme ta domin mu ɗora aiki kamar yadda ake ɗorawa, kuma yau da gobe a hankali a hankali Allah ya yi ikon sa mu ka zama ma’aurata gaba ɗaya.

Abdul Kafinol da amaryar sa, Maryam Sangandale, a ranar Babbar Sallah da ta gabata
Abdul Kafinol da amaryar sa, Maryam Sangandale, a ranar Babbar Sallah da ta gabata

Fim: Kwanan nan an ga hotunan ku na cikar ku shekara biyu da zama ɗaya. Me za ka ce dangane da wannan tsawon lokaci da ku ka ɗauka a matsayin ma’aurata?

ABDUL KAFINOL (murmushi): To, shekaru ne wanda ba zan taɓa mantawa da su ba, tunda shekara ta farko za a ce zaman ka da iyalin ka lafiya lau har a tafi shekara ta biyu lafiya lau, to ka ga abu ne wanda ba zan taɓa mantawa da shi ba a rayuwa wanda kuma ina fatan a ci gaba da ɗorewa a haka, kamar yadda mu ke zaune lafiya mu gama lafiya, ko ta binne ni ko na binne ta. Wannan shi ne fata na.

FIM: Bayan auren ku, ka bar Maryam Sangandale ta ci gaba da waƙa ko ka dakatar da ita?

ABDUL KAFINOL: A’a, har gobe ta na yin aikin ta na waƙa; za ta fita aikin ta, ni ma zan fita aiki na.

FIM: A zaman ka da Maryam, wane abu ne ta yi maka wanda ba ka iya mantawa da shi? 

ABDUL KAFINOL: E to, abin da na ke tunawa kuma ba zan manta ba shi ne a yayin da mu ka haɗu ba wani rufa-rufa, ban rufe mata ba ba ta rufe mani ba. Ba ƙarya a cikin al’amuran mu, haka mu ka ƙulla zamantakewar mu. Idan ina da shi ina da shi, in ba ni da shi ba ni da shi. In zan iya zan iya, in ba zan iya ba ba zan iya ba. To wannan shi ne ya ke riƙe mu a zamantakewar mu ta aure.

Karanta kuma  Yadda Adam Zango ya so ya auri Ummi Rahab – Yasir Ahmad

FIM: Ko nan gaba ka na ganin za ka iya ƙara aure?

ABDUL KAFINOL: Ai ka san ƙara aure ra’ayi ne. Ni dai a zahirin gaskiya tun kafin na yi aure ma, tun kan in san wadda zan aura, ni na mace ɗaya ne gaskiya.

FIM: Mijin-ta-ce ne kenen?

ABDUL KAFINOL (dariya): Ta ma ce ai!

FIM: ‘Ya’yan ku nawa zuwa yanzu?

ABDUL KAFINOL: To, kusan in ce zuwa yanzu ba mu samu ƙaruwa ba, ko in ce mun samu amma aka ɗan samu akasi, irin yadda ake cewa an yi ɓari ko? To gaskiya ɓari aka yi. Yanzu dai mu ke ta neman Allah ya ba mu in-sha Allahu.

Harkar industiri ta na amfani da cewa sai ka kai sannan za a yi da kai,” inji Abdul Kafinol
Harkar industiri ta na amfani da cewa sai ka kai sannan za a yi da kai,” inji Abdul Kafinol

FIM: Wane abu ka fi so a yi maka a ɓangaren abinci?

ABDUL KAFINOL: A ɓangaren abinci na fi so maiɗaki na ta yi min irin salak a haɗa shi da lemon tsami, a barbaɗa masa ɗanɗano da tumatur da albasa, to ni magana ta ƙare!

FIM: Na ga kuma kamar har yanzu ba ka daina cin abincin waje ba, wato na sayarwa, ko?

ABDUL KAFINOL: A’a, ai ni tun da na yi aure ba wani abu da na ke saya a waje, ai gida kawai na ke yi. Kai, wallahi ma in gaya maka, tun da na yi aure idan na ci abincin waje ji na ke ba ya min daɗi.

FIM: Akwai wani abu da za ka iya bayyana wa mutane kan alfanun auren ‘yan cikin wannan masana’anta?

ABDUL KAFINOL: Kamar yadda na gaya maka cewa yawanci idan aka tashi yin aure ba a buɗe gaskiya kowa ya fitar da halayen sa, hali na kaza halin ki kaza, ina da shi ba ni da shi, to yawancin abin da ya ke damun ‘yan industiri gaskiya ƙarya ce, za a yi ta nuna ana da shi alhalin ba a da shi. To yayin da aka yi auren nan ita fa kallon mai shi za ta yi maka, to yayin da ka ce babu ba za ta yarda ba. To yawanci gaskiya abin da ya ke kashe aure kenan, ba ma a industiri ba, gaba ɗaya abin da ya ke faruwa kenan. Kuma wannan shi ne abin da za a cire a cikin harkar aure gaskiya.

FIM: Ka na da wani saƙo zuwa ga masoyan ka?

ABDUL KAFINOL: Ina yi wa masoya na fatan alkairi, kuma masu son su ji waƙoƙi na na kan sa su a kan shafi na na YouTube; duk mai so sai ya je can ya nemo “Abdul Kafinol”, in-sha Allahu zai ga ya na ke ciki da sauran abubuwa na ko waƙoƙin da na saka sabbi.

Sannan akwai sabbin waƙoƙi ma da zan saka kwanan nan in Allah ya yarda.

FIM: Ya batun album fa nan gaba?

ABDUL KAFINOL: To da yake ka san cewa yanzu kaset ɗin ma ba a saya sosai saboda zuwan waya da abubuwa, to gaskiya yanzu ko zan yi album ma a YouTube zan yi kamar yadda kowa ya ke sakawa a can. To duk wanda ya ke da buƙata sai dai ya je can ya ji.

Abdul Kafinol ya ce sirrin nasarar auren sa da Hajiya Maryam shi ne babu ƙarya a cikin zamantakewar su
Abdul Kafinol ya ce sirrin nasarar auren sa da Hajiya Maryam shi ne babu ƙarya a cikin zamantakewar su

FIM: Mun gode.

ABDUL KAFINOL: Ni ma na gode. Sannan a ƙarshe ina yi muku fatan alkairi. Allah ya sada mu da alkairi a ko da yaushe.

Mun dauko muku wannan hirar sukutum daga fimmagazine
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?