Uncategorized

Abubuwa biyar da ke haddasa matsalar rashin karfin mazakuta

Abubuwa biyar da ke haddasa matsalar rashin karfin mazakuta:
Akasarin maza masu fama da matsalar rashin karfin mazakuta su kan kasance cikin boye halin da suke ciki.
Wasu daga cikin dalilan da ke sakawa maza ba sa iya fitowa su bayyana sun hada da al’adar jin kunya da ke tattare da batun a cikin al’umma, wanda ke sa a rika tunanin za su fuskanci tsangwama, da rashin ganin kima da kuma tsegumi idan suka fito suka fada wa abokan zamansu ko kuma wasu mutane daban.
Sakamakon haka, su kan rika fama da wannan matsala a boye su kadai inda daga karshe hakan kan sa su shiga halin tsananin damuwa, da fargaba da sauran abubuwa da firgici kamar yadda bbchausa na ruwaito
Hakan kuma na kara sa matsalar mazakutar tasu ta kara ta’azzara, saboda maza masu fama da irin wannan matsala kan fara jin tsoro har ma da kauracewa duk wata mu’amala da ta shafi yin jima’i da abokan zamansu.
Hakan na haramta wa abokan zamansu yin duk wata mu’amala ta jima’i, wadda idan babu wata yarjejeniya a kai ya kan haifar da lalacewar aure da dangantaka.
Bincike ya nuna cewa maza masu shekaru daga tsakanin 18 zuwa 35 na da kashi 15 bisa dari na matsalar rashin karfin mazakuta, yayin da masu shekaru 40 zuwa sama ke da kusan kashi 40 bisa dari na matsalar.
Saboda haka, Dakta Rasheed Adedapo Abassi, wanda ya kammala karatunsa a makarantar koyon aikin likita ta Yale a Amurka, da kuma ya samu gogewar aiki a fannin kula da lafiyar maza na shekaru 19 ya bayar da wasu shawarwari kan abubuwan da suke haddasa matsalar da kuma wasu hanyoyin kariya da waraka daga cutar rashin karfi mazakuta.
Mece ce matsalar rashin karfin mazakuta (ED)?
Erectile dysfunction (ED) matsala ce wacce namiji ba zai iya samun cikakken karfin tsayawar mazakutarsa na tsawon minti 15 ba.
“Ya kamata a ce kowane lafiyayyen namiji ya kasance yana da karfin tsayawar mazakuta da safe, idan namiji yana rike karfin mazakutarsa na dan lokaci kankani ne ko kuma bai isa ya sa shi iya shiga jikin abokiyar zamansa ba; wannan alamun farko ne na matsalar rashin karfin mazakuta,” in ji Dakta Abassi.
Mene ne ke haddasa matsalar?
Akwai abubuwa da dama da kan haifar da wannan matsala ta rashin karfin mazakuta, amma saboda wannan makala, za mu kawo manyan abubuwa biyar ne da ke haifar da wannan matsala.
1.Rashin sinadarin da ke kunshe da kwayoyin halittar mazakuta (hormone)
Hormone wani sinadari ne a jikin namiji da kan ba shi damar samun zama cikakken namiji ko kuma mai karfin mazakuta, kana shi kuma sinadarin da ke sa mace ta iya daukar ciki da kuma sauran abubuwa da kasancewa cikakkiyar mace shi ne estrogene.
Ba kamar maza ba, sinadarin estrogene a jikin mata kan ragu sosai daga shekara 50, yayin da a bangaren maza duk da cewa sinadarin testosterone ba ya taba kafewa, amma wasu matsaloli kan haifar masa da nakasu.
2.Tsananin sukewa da tunani
Tsananin sukewa da tunani daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalar rashin karfin mazakuta. Ya kan faru daga rasa aiki, ko matsalar rashin kudi da kuma zamantakewar aure da sauran damuwa da tsananin tunani da sauran abubuwa ka haifar.
Abubuwan da suke haifar da sukewa da sun banbanta da motsa jiki, saboda idan kana motsa jiki zuciya ta kan harba jini ta ko ina a zagayen jikin dan adam.
3.Rashin motsa jiki
Ba za a iya bai wa wannan muhimmanci ba idan ana batun yin kanda-garki daga kamuwa da matsalar rashin karfin mazakuta; akwai bukatar namiji ya muhimmantar da al’adar motsa jiki na akalla minti 30 a ko wace rana.
“Za ka iya fada min ko wane irin motsa jiki ne nake bai wa marasa lafiyana shawara a kaI? Jima’I mai kyau.” Dakta.Abassi ya bayyana. “Ina bayyana gaskiyar abubuwan da bincike ya tabbatar”.
4. Cikakken jima’i mai kyau:
Dakta Abassi ya bayar da shawarar cewa ya kamata namiji ya fitar da maniyyi sau 21 a cikin wata guda; ya bayyana cewa cikakken jima’i mai kyau zai taimaka wajen inganta lafiyar ma’ajiyar ruwan da ke kunshe da maniyyi, tare da kare shi daga kamuwa da cutar kansa daga baya.
5.Rashin samun tsaftataccen ruwan sha:
Wannan ka iya zuwa da mamaki ga wasu mutane amma kamar yadda Dakta Abassi ya bayyana, “shekaru kafin shekarar 2000 karin wasu mutane na samun tsaftataccen ruwan sha wanda ke kunshe da sinadaran macronutrients.
Rashin samun tsaftataccen ruwan shan kan kara haifar da matsalar rashin mazakuta ko haihuwa ga maza.
“Ya kuma ci gaba da cewa “gwamnati ce ke da alhakin tace ruwan don amfanin jama’a ta hanyar amfani da sinadarai kamar su fluoride, da calcium, da selenite wadanda duk suna bayar da gudumawa wajen samar da lafiyayyen maniyyi ga maza”.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button