Kannywood

Kungiyar Malaman Tsangaya ta bukaci a dakatar da Fim din “A duniya”

Shirin Fim din A Duniya kenan

A yanzu haka dai wata Sabu war rigima ta bullo tsakanin jarumi kuma Furodusa Tijjani Abdullahi Asase da kuma wata kungiyar makarantun Tsangaya, sakamakon zargin sa da su ke yi da cewar, ya ci mutuncin Malamai da kuma makarantun na Tsangaya a cikin fim din sa mai dogon na “Zango A duniya”.

Malaman dai sun tura masa da sakon cewar lallai ya gaggauta yin gyara a cikin wasu bangarorin da aka yi a cikin fim din, wanda ya tabo tsarin makarantun Tsangaya.

A cewar Kungiyar, abun da aka yi, ya yi kama da cin mutuncin addini da kuma Malaman, don haka idan har abin ya ci gaba za su dauki mataki, domin ba za su zuba ido suna kallo ana yin izgili da sunan makarantun Tsangaya ba, kan haka ne kungiyar ta yi kira ga Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, da lallai ta dauki matakin Dakatar da fim din don kada ya zama wata fitina.

Sai dai da wakilin Dimukaradiyya ya nemi jin ta bakin Tijjani Asase dangane da sakon da Malaman Tsangayar suka fita ya ce “Ni abun mamaki ya ba ni, domin abu ne da na yi shi bisa doron bincike, kuma wasu abubuwan ma ba za su fadu ba, domin na yi zaman gidan Mari don haka na san abubuwan da su ke faru wa a ciki, abin da muka yi a cikin fim din A Duniya, fadakar wa ce, da kuma isar da sako, don haka, ba mu yi ba domin mu bata wasu ko wani Rai ba,” inji shi.

Asase ya cigaba da cewa, “Ni Musulmi ne, kuma duk abin da zai kawo cin mutunci ga addini na ba zan yi shi ba, don haka, ba mu yi da wata manufa ba, Amma idan wani yana ganin haka to fahimtar sa ce. ” a cewar shi.

Dangane da kalmar In da Rabbana da wasu Malamai suka soke shi a kan ya gyara kuwa cewa ya yi

“Shi wanda ya yi mun wannan maganar, na tura masa In sha Allahu, ya yi mun gyara, amma har yanzu bai ba ni amsa ba, don haka ina kira ga Malamai da su tsaya matsayin su na Malamai ba su rinka shiga hurumin da ba na su ba. Domin su masu gyara ne, don haka, bai kamata su rinka kafirta mutane da kokarin kai su wuta ba. ” A cewar Tijjani Asase.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?