Kannywood

Bani Da Aboki ko Babbar Abokiya Nice Abokiya kaina – Nafisa Abdullahi

Fitacciyar jarumar Kannywood wanda ta shahara wajen fitowa a finafinai masu daukar hankali da nishadantarwa, Nafeesat Abdullahi ta bayyana cewa a kullum ita tana duba abinda zai amfanar da ita ne a ruwa kuma hakan da take yi yana haifar mata da daukaka da ci gaba matuka.
Nafeesat ta shahara matuka a farfajiyar Kannywood wanda manazarta farfajiyar ke ganin tana daga cikin fitattun yan wasan da farfajiyar finafinan Hausa ta taba yi.
A hira da tayi da PREMIUM TIMES, jarumar ta bayyana dalilin da ya sa ta rungumi karatun koyon aikin daukan hoto wanda take yin sa a kasar Birtaniya.
” Daukan hotuna na daga cikin sana’a ta kuma ina matukar son daukar hotuna musamman na abubuwan ban sha’awa, abubuwa masu kayatarwa. Wannan shine dalilin da ya sa na rungumi daukan hoto da koyar da shi.
” Sannan kuma dalilin da ya sa ake yi mini ganin jaruma a Kannywood bai wuce maida hankali da na yi a sana’ata ba. Babu siddabaru ko wani abu da ban da ya kaini ga matsayin da nake. Maida hankali ne da kwazo da na saka shine kawai siurri na. Duk abinda na saka a gaba shi nake yi kuma nakan maida hankali ne matuka.

Nafisa Abdullahi

Bayan haka Jaruma Nafeesat ta ce yi karin haske game da matsalolin da farfajiyar Kannywood ta ke ciki ” Wannan ba sabon abu bane, matsaloli a farfajiyar fina-finai sukan bijiro a koda yaushe. Na mu aka sani, su ma sauran haka su kan yi fama da shi, ba a dai sani ne.
” Amma duk halin da aka shiga in shaAllahu za mu fito da karfin mu a Kannywood. Muna ma kokari domin farfajira ita take goya kanta, babu tallafi da take samu daga gwamnati.
Game da wadanda take jindadin fitowa a finafinai tare Nafeesat tace ba ta da wanda ya fi mata duk jarumin da ya iya taka rawa mai kyau a fim tana son taka wasa da shi ko ita a koda yaushe.
” Bani da wani babban aboki ko babbar abokiya a Kannywood, Ni ce babbar abokiyar kai na, Na san hakan zai baku mamaki ko?
Sannan abinda yake birgeni a rayuwa shine idan naga yara kanan na yi mini lale-lale maraba suna farinciki da abinda na ke yi, abin na yi mini dadi matuka, yakan faranta mini rai sosai.
Akarshe ta yi magana kan kamfanin Tpumpy wanda ita jakadiyar Kamfanin ne.
” A dalilin wannan Kamfani, na mallaki kadarori sannan kuma duk shekara suna bani sabuwar mota da kuma kuma albashi a matsayina na jakadiyar Kamfanin.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button