Kannywood

Yadda Hadiza Gabon ta zama Uwar Marayu

Yayin da Jaruma Hadiza Gabon ke karba kyauta daga daya daga cikin malaman makaranta

Malami ya ce ‘yan fim ba gafalallu ba ne
WATA makaranta a Kaduna ta karrama fitacciyar jaruma Hadiza Gabon da muƙamin ‘Uwar Marayu’.
 
Makarantar, mai suna ‘IRFA International School’ da ke Gwanja Road, Malali GRA, cikin garin Kaduna, ta naɗa jarumar da muƙamin ne a lokacin wani taron karrama wasu muhimman mutane da kuma ciyar da ɗalibai gaba da makarantar ta gudanar a watan Ramadan da ya gabata.
 
‘IRFA International School’ dai makaranta ce ta Islamiyya da boko tare da haddar Alƙur’ani.
 
A lokacin da wakilin mujallar Fim ya ziyarci makarantar, daraktan makarantar, Malam Awwal Muhammad Musa, ya bayyana jin daɗin sa kan gudunmawar da Hajiya Hadiza Gabon ke bayarwa ga al’umma, har ya ja hankalin al’umma da su daina kallon mata masu harkar finafinan Hausa a matsayin marasa tarbiyya ko gafalallu a cikin jama’a.
 
Malamin ya bayyana godiyar sa tare da yabo ga Hadiza saboda yadda ta dage wajen tallafa wa gajiyayyu da marayu, ya ce yin hakan ba ƙaramin al’amari ba ne a Musulunci.
Daraktan ya ce a lokacin da aka yi wancan taro, Hajiya Gabon, a bisa jinƙai da tausayi irin nata, ta ɗauki alƙawarin ɗaukar ɗawainiyar karatun yara 20 marayu na makarantar, al’amarin da zai fara aiki a kowane lokaci na wannan watan Sallah.
Ɗaliban ‘IRFA International School’ a lokacin taron. Hoto na can sama kuma Hadiza Gabon ce ke karɓar lambar yabo daga hannun daraktan makarantar, Malam Awwal Mohammad Musa

Ya ce sakamakon wannan karamci na jarumar ne ya sanya hukumar makarantar ta karrama ta da lambar yabo tare da tabbatar mata da muƙamin ‘Uwar Marayu’ ta ‘IRFA International School’.
 
Da ya ke jaddada kiran sa ga al’umma a lokacin hirar tasa da wakilin mu a ofishin sa, Malam Awwal Mohammad Musa ya ce, “A gani na, bai kamata mu riƙa kallon ‘yan fim a matsayin mutane zubabbu ko mutane marasa tarbiyya ba, a’a, su ma ‘yan’uwa mu ne. Abin da su ke yi sana’a ne, duk inda su ka yi kuskure a gyara.
 
“Ba aikin da ba za a yi kuskure a cikin shi ba; ko aikin gwamnati ba a nuna mutum a ce ga shi nan ya kwashi kuɗi ko ya saci kuɗi, shi ma ai ɓarna ne, kuma in ya yi ɓarnar ai ka ga malamai su na hawa mumbari su gyara mashi, su ce a guji cin haram a guji kaza a guji kaza. To su ma ‘yan fim a gyara masu aikin su sana’a ne.
 
 
“Ni ina kallon shi a matsayin sana’a, kuma sana’ar da in aka inganta shi na farko zai rage masu faɗawa cikin halaka, ga kuma hanyar samun kuɗin shiga. Na biyu, zai maida su mutane. Na uku, zai rage wa ƙasa zauna gari banza.
 
“Da yawa, in na ci gaba da lissafa maka za ka ga amfanin shi ya fi rashin amfanin yawa. Kuma illar nashi ma idan mutane da malamai su ka dinga faɗakarwa za ka ga an gyara.”
 
A ƙarshe, shugaban makarantar ya bada shawarar cewa duk inda aka ga wata matsala a harkar finafinan Hausa, to a dage a inganta harkar don ta na rage wa ƙasar gaba ɗaya rashin aikin yi da zaman banza.
 
 
Ɗaliban makarantar da malaman su a wajen taron

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button