Kannywood

Jarumi Sahabi Na Kwana Casain Yayi Martani Kan Masu Aibanta Halittarta Matarsa

Yau ne Majiyarmu hausaloaded ta samu labarin cewa Aliyu hussein wanda anka fi sani da sahabi a cikin shirin Kwana Casain yayi martani kamar yadda Rabiu Biyora ya wallafa a shafinsa da cewa wannan jarumi yayi martani ga masu ganin bai dace ya auri hassana ba.
Ga abinda ya wallafa kamar haka
SUNANA ALIYU HUSSEIN….
Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aibata halittar ta, sun san ni bayan dana zama SAHABI a cikin shirin Kwana Chasa’in, basu sanni a lokacin da nake Aliyu ba….
Alhamdulillah Hassana ta kaunaceni a lokacin da ni ba kowan kowa bane, lokacin da hatta a unguwarmu ba kowa bane yasan dani, don haka ne nima na rike alkawarin ba zan iya rabuwa da Hassana ba, koda kuwa me na zama a wannan duniyar…

Ango Aliyu Hussein wanda anka fi sani da Sahabi kwana casain

Akwai Yan’mata masu yawa da suka nuna kauna gareni a yanzu bayan dana zama SAHABI, to amma anya kuwa Aliyu suke so, kodai Sahabin Kwana Chasa’in suke so…?
Soyayya ta tsakani da Allah Hassana ke yimun, haka nima dai soyayya ta gaskiya nake mata, ni da ita ba kyale kyale muka kalla ba…
Ni Aliyu Hussain ina cigaba da yiwa Allah godiya sakamakon kyautar Mata Hassana daya bani, ina kallon kyawunta kwatankwacin sarauniyar kyau ta duniya, ina addu’ar Allah ya hadani da Matata Hassana a aljana…..”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

  1. Alhamdllahi naji dadin wannan maganar ina son mutum maikishin iyalinsa aduniya kada kumeya Zama karka duba kyau dai kayi lakari da me take sonka don Allah ko dai don abinduni Kuma kowa arayuwa burinssa yasami mata gari Allah yasamu dace ameeeen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button