Labarai

An yi garkuwa da malamai da ɗalibai a makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya

Rahotanni da ke fitowa da Zariya a jihar Kaduna na cewa wasu sun auka wa makarantar kuma sun yi garkuwa da mutane a ƙalla mutum takwas ranar Alhamis da daddare.

Rahotannin na cewa cikin mutanen da aka sace akwai malamai da ɗalibai da iyalin wani malamin makarantar.

Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito, Wasu rahotannin na cewa ɗalibi ɗaya ya rasa ransa sanadiyyar harbin bindiga yayin da wani ya samu rauni.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar wa BBc faruwar lamarin kuma ya ce jami’an tsaro sun yi gaggawar zuwa makarantar don tarwatsa maharan.

Sai dai bai bayyana adadin mutanen da ka yi garkuwa da su ba.

Makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic ba ta da tazara sosai da sansanin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?