Labarai

‘Yan Bindiga Hudu Sun Tuba Sun Ajiye Makamai Da Maido Da Shanu 45 Da Suka Sata A Katsina (Hotuna)

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Wasu daga cikin shugabannin yan bindiga da suka addabi jihar Katsina da sace-sace mutane da kisan gilla sun ajiye makaman su a yau Alhamis a helkwatar rundunar yan sanda ta jihar Katsina.

Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamishinan yan sanda Sanusi Buba ya ce, shugabannin da suka mika wuya da ajiye makaman akwai Sale Turwa da Mani Turwa da Ado Sarki da kuma Sani Mai Daji, sun fito a Dajin garin Illela da ke cikin karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

Kwamishinan yan sanda ya cigaba da cewa sun maido shanu arba’in da biyar da manyan bindigogi na (Machine Guns) guda biyu da bindiga kirar Ak47 guda ashirin da hudu da alburasai na manyan bindigogi guda dari da goma da alburasai guda tis’in da biyar.

Sanusi Buba ya kara da cewa mika wuya da wadannan shugabanni yan bindiga yana cikin kokarin da rundunar yan sanda ta jihar Katsina da kuma sauran jami’an tsaro da ke yaki da bindiga domin kawo karshen satar Mutane da Kashe-kashen yan bindigar.

Ga kadan daga cikin hotunan nan.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?