Kannywood

Ummi zee zee Tayi Martani Mai Zafi Zuwa Ga Yan Arewa Musulmai Akan Damfararta Da Ankayi Naira Milliyann 450

A yau ne jaruma ummi zee zee tayi rubutu bayan wanda ta nuna zata iya kashe kanta akan kuncin rayuwa da ta shiga wanda ta nuna an damfareta kudi masu yawan da sunka kai naira miliyan 450 inda tayi godiya da kuma nuna bacin ranta sosai akan irin yadda musulmai yan arewa nayi mata.

Inda ta wallafa a shafinta na sada zumunta kamar haka

Salam to nigerians ina son kuban dama in gode muka abisa jaje da kukamin ta hanyar kirana a waya da aiko min da text dangane da damfara na da akayi na kudi masu yawa naira million dari hudu da hamsin Wanda wani inyamuri dake lagos ya damfareni akan business da zamuyi dashi na Saye da sayarwa na DANYEN MAI.to sai dai akwai abu daya ban mamaki Wanda wasu makiya na saboda hassada da jahilci suke ganin wai ba wani damfarana da akayi,to akan me zanyi karyar an cuceni in nayi karyar aljanna za a ban koko zunubai na za a yafemin da zanyi karya akan hakan ?to a gaskiya hausawa yana da kyau mu koyi son junan mu domin ko wani musulmi dan uwan musulmi ne,sai da aka damfareni na gane arnan nigeria wallahi sunfi musulman nigeria tausayi .abunda yasa nace haka shine :da aka damfareni akwai wani page mai suna @instablog9ja sunyi posting din damfaran da akamin ammah da na shiga page din wani abun mamaki da mai page din da followers dinsa wallahi arna ne yawancinsu ammah kowa a page din sai suka hau yimin addu’ar allah ya sakamin cutana da akayi wasu kuma suka dinga ban hakuri wasu kuma direct suka dinga kirana suna min jaje,ammah anan arewa kuwa duk wani page da akayi posting damfaran da akamin to kowa sai dai ya hau zagina to naji haushi sosai,bawai haushin zagina da akeyi naji ba ,no haushin danaji shine ina musulma masifa ta fada kaina ammah ace sai arna ne zasu jajantamin musulmai kuma sai zagina kawai suka dinga yi wannan wani irin karshen duniya ce muka zo ace musulmi baya tausayawa musulmi dan uwansa in kaddara ta fada masa ?wel allah ka shiryi duk wani musulmi mai irin wannan mummunar zuciyar ! Sannan ina mika godiya na ga manyan mutane masu gidana Wanda suka dinga aikomin kudi ta account number na domin irin rage asara .nan ba da dadewa ba inna nemi izinin manyan mutanen zanyi posting sunayensu da kowa kudin daya ban domin masoyana so tayani gode musu .sannan ina yiwa kanwata @hasina_dan_chaina godiya data zo har kano ta takamin birki ta hanani aikata SUICIDE danace zanyi.tabbas naso na aika suicide din saboda abu 3 yanzu suna damuna na 1.mutuwan babana na2 ina son wani mamaci na3 damfaran da akamin.a karshe kuma ina tuba ga Allah dangane da kaina dana so na kashe.”

 

View this post on Instagram

 

A post shared by ummi ibrahim zeezee (@ummizeezee)
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?