Labarai

Hoton matar da ake zargin ta kashe kishiyarta ta kona ta, Kotu ta sa a Daureta

Kotun Magistre dake Minna ta sa a daure wata mata ‘yar Kimanin shekaru 24 da ake zargi da kashe kishiyarta ta kona ta.

Matar me suna Amina Aliyu ta kashe Amaryar Mijinta, Fatima Aliyu da tabarya inda kuma ta koneta a raran 23 ga watan Maris.

kamar yadda Hutudole na ruwaito.An gabatarbda amina a kotu tare da Zainab Aliyu da A’isha Muhammad, sai kuma Fauziyya Rabiu.

Ana zargin wanda aka gurfanar da ita tare dasu wajan taimaka mata aikata laifin. Me shari’a, Nasir Mu’azu ya nemi a tsaresu a gidan canja hali da kuma daukaka ci gaba da shari’ar zuwa 27 ga watan Afrilu.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?