LabaraiSports

Bidiyo : Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa

“Yau mun samu takarda daga hukumar da ke gudanar da wasanni ta Premier League a Najeriya cewa, sun yarda, shi ma Ahmed Musa ya amince cewa zai sake dawowa ya yi wasa a League din Najeriya,”
Kyaftin din kungiyar Super Eagles ta Najeriya Ahmed Musa, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, kamar yadda shugabanta Surajo Shu’aibu Yahaya ya tabbatarwa da VOA.
Tun a karshen makon da gabata ake ta rade-radin cewa Musa wanda ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudiyya a watan Oktoban bara na shirin komawa murza leda a gasar Premier League ta Najeriya.
“Yau mun samu takarda daga hukumar da ke gudanar da wasanni ta Premier League a Najeriya cewa, sun yarda, shi ma Ahmed Musa ya amince cewa zai sake dawowa ya yi wasa a League din Najeriya,” in ji Yahaya.
Ya kara da cewa, “kuma mun rubuta musu amsa cewa, mun amince, mun yarda da wannan tagomashi da Allah ya yi mana. Don haka, muna yi masa barka da zuwa.”
A cewar shugaban kungiya, Kano Pillars, Plateau United da Eyimba United na daga cikin kungiyoyin da suka yi zarwacinsa.
Karin bayani akan: Ahmed Musa, Premier League, AFCON, Super Eagles, Nigeria, da Najeriya.
“Amma Allah da ikonsa, ya yarda ya amince zai zo kungiya ta Kano Pillars.” Yahaya ya ce.
Da ma dai Musa daga Kano Pillars wacce ke arewacin Najeriya ya fito idon duniya abin da wasu ke ganin kome ya yi.
Tun bayan barin shi Saudiyya, Ahmed bai samu kulob ba, yayin da rahotonni suke nuna cewa ana kan tattaunawa da shi da wasu kungiyoyin kasashen ketare.
Wasu da dama sun yi ta sukar kocin Super Eagles Garnet Rohr saboda gayyatar Ahmed da ya yi zuwa wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da Najeriya ta buga da Benin da Lesotho a kwanan nan, suna masu cewa, hakan bai da ce ba, lura da cewa ba shi da kulob.


Kamar yadda voa hausa na ruwaito.Amma Rohr ya kare kansa, yana mai cewa dan wasan zai zama kamar garkuwa ne ga ‘yan wasan na Najeriya tare da kara musu kaimi.
Musa dan shekara 28, ya bugawa CSKA Moscow a matsayin dan wasan aro inda daga nan ya nausa Leicester City ta Premier Leagu din Ingila, ya kuma yada zango a Al Nassr a karshe.
Ita dai kungiyar ta Al Nassr ta ka da kungiyoyin nahiyar turai da dama a lokacin da ake zawarcin dan wasan, wanda tauraruwarsa ta haska a gasar cin kofin duniya ta 2018 da aka yi a Rasha.
Ya bugawa Al Nassr wasanni 58, ya ci kwallo 11 tare da tallafawa wajen zura kwallo 14, ya kuma taimakawa kungiyar lashe kofin gasar Saudi Super Cup a 2019.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button