Amurka Na Sane da Masaniyar karshen Shugaba Idris Daby


Majiyarmu ta samu wannan tsokaci daga wani jajirtacen marubuci malam Yasir Ramadan gwale inda ya ke cewa.
“Amurka ta san abinda zai faru a Chadi tuntuni shi yasa a makon da ya gabat suka gargadi dukkan ‘yan kasarsu da su fice daga Ndjamena domin gudun abinda zai je yazo. A takaice dai Amurka suna da masaniyar karshen abinda zai faru da Shugaba Daby. Domin yadda ya fito ko yayi nasara ko ai nasara akansa.
Shugaban kasar Chad Idris Daby Itno ya rasu yau bayan a jiya an bada sanarwar lashe zabensa na Shugaban kasa karo na shida a wa’adin mulki na shekara biyar sababbi fil bayan ya shafe sama da shekaru talatin yana jan ragamar kasar.
Daman Bahashe yace makashin maza, maza kan kashe! Idris Daby Itno jajirtaccen Soja ne da bai da tsoro, kasancewarsa aboki na kurkusa da Marigayi Kanar Muammar Qazzafi yasa ko yaushe yake cikin shirin ko ta kwana, saboda Idris Daby na daga cikin shugaban da kusan duk shekara sai anyi yunkurin yi masa juyin mulkin da baya cin nasara.
Daby ya jima yana zargin wasu hannaye a Sudan da Kamaru da BarkinaFaso da kuma Amurka wajen yunkurin kifar da Gwamnatinsa. Tunda aka barke kasar Libya makamai suka watsu a hannun ‘yan tawayen kasar Chad hankalin Idris Daby bai taba kwanciya ba, shi yasa ko da yaushe ake ganinsa a fagen daga wajen karfafawa sojojin kasar guiwa wajen fada da ‘yan tawaye.
Daby cikakken dan kama karya ne, wanda ya hana kowa sakat a kasar, magoya bayansa da ba su da wani zabi sai dai subi abinda yake so sune kadai suke walwala, ya tsanantawa ‘yan adawa kwarai da gaske, ya murkushe su ta yadda ana adawa ne kawai dan a nunawa duniya ana demokaradiyya a kasar.
Yau Allah ya kawo karshen Shugabancin Idirs Daby Itno na tsawon fiye da shekaru talatin. Za a tuna da Daby wajen jajircewa akan yaki da ‘yan ta’adda musamman Boko Haram da ya shige gaba wajen fatattakarsu daga iyakokin kasarsa, bugu da kari an kashe shi wajen kare kasarsa daga mamayar ‘yan tawaye. Allah ya jikansa ya gafarta masa.
Yasir Ramadan Gwale
20-04-2021″