Labarai

Za a kyale sojoji mata su rika sanya ɗan kamfai a Switzerland

Kafafen watsa labarai a Switzerland sun ce kasar za ta soma kyale sojoji mata su rika sanya dan kamfani da sauran kaya irin su singileti a karon farko a yunkurin kara samun masu son shiga aikin soja.
A halin yanzu, kakin sojan da ake bai wa sojoji sun hada ne kawai da dan kamfani na maza.
Daga watan gobe za a soma bai wa mata dan kamfani irin biyu, wanda zai dace da lokacin zafi da wanda zai dace da lokutan sanyi.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Mata su ne kashi 1 cikin dari na sojojin kasa na Switzerland, sai dai kasar tana fatan samun kashi 10 cikin dari na mata da za su shiga aikin soja nan da 2030.
Marianne Binder, mamba a majalisar kasa ta rundunar sojin Switzerland, ta ce bai wa mata damar sanya dan kamfan da ya dace da su zai karfafa gwiwarsu wajen shiga aikin soja.
“An dinka tufafin ne domin su dace da maza, amma idan ana so mata su ji dadin aiki a rundunar sojin kasa, ya kamata a dauki matakan da suka dace,” in ji ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button