Labarai

‘Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara

Al’ummar garin Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sun gamu da taskun ‘yan bindiga, wadanda rahotanni suka ce sun kona rabin garin da dukiya mai dimbin yawa, kuma suka yi awon gaba da mutane fiye da sittin.

Hakan ya auku ne yayin da matsalar satar ‘yan makaranta ta fara auka wa daliban makarantun jeka-ka-dawo a garin Runka na jihar Katsina.

Yanzu haka jama’ar garin sun tsere, “matsalar nan ta yi mana nauyi, ko shekaranjiya da jiya ma sun kawo mana hare-haren nan. Sun kone mana gari da motoci da shaguna da gidaje, kudan rabin garin sun kone shi,” in ji wani dan garin da muka biye sunansa.

Ya ci gaba da cewa ba a samu asarar rai ba amma ‘yan bindigar sun harbi wani kuma yanzu haka yana asibiti a kwance.
BBChausa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button