Labarai

Yadda Zaku Training Din NYIF Gobe Litinin Domin samun Daga Kudi Daga 3 Million -500k

Tsarin Bawa Matasa Ranche Na “Nigeria Youth Investment Fund” (NYIF) Za Su Fara Bawa Mutane Training A Manhajar YouTube A Gobe Litinin
…. Wa ‘yanda suka kammala shigar da bayanansu, aka kuma turo musu da sakon yin Training ta Gmail dinsu ne kadai zasu yi Training.
A nutsu a karanta da kyau domin a amfana, tare da yiwa al’umma share domin suma su amfana.
Wa ‘yanda basu kammala cika bayanansu ba, da wa yanda har yanzu baa musu Verified ba, su kara dagewa domin su Kammala dukda har yanzu ana fusktantar Matsalar Network.
Masu ragista da CAC daga Miliyan Ukku zuwa kasa, wa ‘yanda basu da CAC daga Dubu 500K, zuwa kasa zasu iya neman a basu.
A jiya lahadi Tsarin bawa matasa ranche na “Nigeria Youth Investment Fund” (NYIF) suka fara turawa wa yanda suka kammala cika bayanansu da sako ta Gmail domin a fara bawa mutane Training a manhajar YouTube a gobe litinin.
Duk wanda yasan ya kammala cika bayananshi sai ya duba Gmail dinshi, wasu an turo musu wasu kuma sai mako Na gaba, amma wa yanda suka cika da Kamfani mai ragista baa fara turo musu ba, masu Individual aka fara turowa zuwa yanzu.
Idan kowa ya duba sakon nashi ta Gmail zaiga ranar da aka ware mishi domin yayi Training, kowa zai yi training Na tsawon kwana daya ne amma kowa da nashi ranar wasu Monday wasu Talata wasu Laraba wasu Alhamis wasu Jumma’a, sai a lura da kyau a cika dukkannin ka’idojin da suke bukata.
Ana kyautata zaton da zaran mutum ya kammala Training bada dadewa ba zasu turo mishi da kudin da ya nema a bashi.
Me Yasa Har Yanzu Miliyoyin Mutane Sun Kasa Samun Dama Domin Su Cika Bayanansu A Manhajar Bayan Suna Daga Cikin Wa Yanda Zaa Baiwa Bashin Ranchen?

Wannan shine sakon da wanda ya samu nasara zai gani a email dinsa da ranar da zaiyi training

Tun lokacin da aka fara tura wa mutane sakonni domin su cike bayanansu a manhajar daga lokacin network din manhajar ya fara nuna damuwa da matsala saboda yadda Miliyoyin mutane suke ziyartar shafin a kowacce dakika shiyasa har yanzu Miliyoyin Mutane basu iya samun damar saka bayanansu ba, amma a cigaba da gwadawa Inshaallah kowa zai saka, amma hakan yana matukar daukan tsawon lokaci.
Karin Bayani: Yadda Zaka Yi Verified Din Kanka Domin Ka Cike Dukkanin Bayananka a nanMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button