Labarai

Wata Sabuwa: Malam Abduljabbar ya yi watsi da dakatar da muƙabala

Malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya yi watsi da shirin dakatar da muƙabala da kotu ta bada umarnin.
Malam Kabara ya bayyana hakan ne, ta bakin lauyan sa Barista Rabi’u Shu’aibu Abdullahi.
Lauyan ya ce, su ba su samu umarnin kotun ba sai dai kawai a kafafen yaɗa labarai.
Kamar yadda Freedom radio na ruwaito.Ya ci gaba da cewa, ko a baya da kotun ta bada umarnin dakatar da Malam Abduljabbar daga karatu ba a sanar da su ba, sai dai kawai sun gani a kafafen sada zumunta.
“Idan mutane suka lura da odar kotun ko sunan Sheikh Abduljabbar ba bu a jiki, kuma ba a kai masa takardar cewa za a zauna a kotu ba”.
Ya ƙara da cewa, saboda haka su ba sa cikin waɗanda ake yin shari’ar da su a gaban kotun, kuma har yanzu suna nan a shirye domin zuwa muƙabala ranar 7 ga wata kamar yadda gwamnati ta ba su a rubuce.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da wata kotun majistiri da ke Kano ta bada umarnin dakatar da Gwamnatin Kano daga shirin muƙabalar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button