Labarai

Na amince da umarnin kotu na dakatar da muƙabala – Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, zai yi biyayya ga umarnin kotu na dakatar da shirin Muƙabalar malamai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan shari’a na jihar Barista Musa Abdullahi Lawal.
Kamar yadda Freedomradio na ruwaito.Kwamishinan ya ce, wannan Gwamnatin ba ta karya umarnin kotu, saboda haka za ta yi biyayya da umarnin musamman ganin kotun tana da hurumin bayar da shi.
Ya ci gaba da cewa, ai ba daidai ba ne a ce kotu ta bai wa Gwamnatin umarni kuma ta ƙi ba, a don haka yanzu babu batun zaman muƙabala ranar Lahadi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button