Addini

Limaman da za su jagoranci sallar Taraweeh da Tahajjud a masallancin Harami a bana

Hukumomin Saudiyya sun fiter da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.

Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.

Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai zuwa.

Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito.Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasulLimamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.

Babban limamin masallacin Ka’abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.

Ga hotunan limaman da za su ja ragamar sallolin Tarawi da Tuhajjud.

Sheikh Abdul Rehman Al Sudais
Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

Sheikh Maher Al Muaiqly
Sheikh Saud Al Shuraim

Sheikh Yasir Al Dossary

Sheikh Bandar Baleelah
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?