Addini

Irin Mijin Da Ya Kamata A Aura Mai Siffofi kamar haka ~ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Bayan rubutun da na yi yau akan irin matar da ya kamata a aura, da yawa sun nemi na kawo ɗaya ɓangaran wato irin mijin da ya kamata a aura, domin a sami balance,
Shawarwari da ake bawa iyaye da wakilai da mata shine su tantance wanda ya kamata su bawa aure.
A matsayin ka na uba ko waliyyin mace ya kamata kafin ka bawa wani auran ƴarka, ka bincike shi sosai kada a yi gaggawa, abi a sannu domin ƴarka ba abar wasa ba ce, da za ka bayar da ita ga wanda ba a tabbatar da nagarta da mutuncin sa ba.
Akwai siffofin da halaye da ake dubawa ga mutumin da za ka bawa aure, sune :
1. Addini, saboda hadisin Idan wanda kuka yarda da addinisa da halayen sa ya zo neman aure ku bashi, a wannan hadisi an bayyana muhimman siffofi guda biyu na mutumin da za a bawa aure, sune riƙo da addini da halaye masu kyau.
2 Halaye masu kyau, idan kun yarda da halin mutum, ya na da kirki da nagarta za a iya bashi aure, anan an banbanta hali da addini, domin wani yana kula da salla amma baya kula da iyali wani kuma ya na da ilmi amma baya aiki da shi.
3. Sana’a da aikin yi, saboda Hadisin Bukhari na Faɗimatu Bnt Ƙaysi, wanda sahabbai biyu suka fito neman auran ta Mu’awiyya da Abu Jahmin, Manzon Allah saw ya hana ta aure su, shi Abu Jahmin ya na dukan mace, shi kuwa Mu’awiyya a lokacin talaka ne bashi da hali, wannan ya nuna wajibi ne a binciki sana’ar mutum kafin a bashi aure, domin idan ka aurar da ƴarka ga wanda bashi da Sana’a, duk nauyin auran kanka zai dawo,
4. Asalin sa da tushen da ya fito, abincika asalin mutum da tushen sa a lokacin da ya fito neman aure, domin rashin sanin wannan zai iya sawa ayi rufin gida da ɓarawo.
5. Lafiyar sa. Saboda akwai cututtuka da ake ɗauka, ya kamata ko ya wajaba aje ayi bincike gamai da lafiyar maaurata duk su biyun, domin a tabbatar da lafiyar su, kafin aure.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button