Addini

Gaskiya Gwamnatin Jihar Kano Bata Kyautawa Khalifa Sheikh Mahi Inyass Da Sauran Shehunnan Tijjaniyya Ba

Abinda ya faru a gidan gwamnatin jihar dangane da jawabin da Maualan Khalifa Sheikh Mahi Inyass yayi akan Halifancin Muhammadu Sunusi ||, ya jawo cece kuce a tsakanin mabiya darikar tijjaniyya wanda ya jawo har wasu na zargin Shehunnan da suka raka Khalifa da kitsa wannan lamarin.

A zahirin gaskiya wannan abin ba wani ya jawo shi ba sai gwamnatin jihar Kano, domin gwamnati ta gayyaci halifa ne dan ta shirya masa liyafan girmamawa tare da tawagarsa, kwatsam halifa na cikin jawabi sai kwamishinan addinai na jihar Kano Baba Impossible ya tashi a gaban Gwamna Ganduje ya tambayi Halifan Shehu Ibrahim Inyass Sheikh Mahi Inyass cewa, wai shi ya nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin Halifan Shehu Ibrahim Inyass na Nigeria ?

Amma jikan Shehu Ibrahim dan Syda Aisha Inyass Shehu Tijjani Sani Auwalu ya mayar masa da Martani a take inda yace ai wannan ba maganar nan wurin bace dan haka Halifa ba zai yi magana a nan ba.

Bayan haka Halifa yace maganar Halifanci Sai an tuntubi Shehunnai da Mukaddaman Nigeria su zasu yanke hukunci.

Wannan shine hakikanin abinda ya faru, amma da yake gwamnati suna da wata manufa nasu na siyasa, sai suka yanke tambayar da Kwamishina yayi suka yada jawabin Khalifa kadai dan mutane suyi zargin cewa halifa ne dan kansa yayi wannan jawabin ba tambayansa akayi ba, haka kuma suka rubuta suka yadawa manema labarai cewa Halifa ya bayyana cewa ba’a nada Sarki Sunusi a matsayin Halifan tijjaniyya ba.

Gaskiya gwamnatin Kano bata yiwa ‘yan tijjaniyya adalci ba domin wannan abin yaso ya saryar da mutuncin wasu manyan Shehunnan tijjaniyya a idon duniya, dan a zahirin gaskiya wasu da farko sun fara zargin Shehunnan da suka raka Halifa da kitsa wannan lamari dan neman fada, alhali ba su shirya hakan ba kuma ba su san za’a shirya hakan ba.

Allah ya kiyaye gaba amin.

Daga : fatyanul Islam of Nigeria
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?