Labarai

Ganduje ya yi watsi da shawarar Sarkin Musulmi kan muƙabala

Ganduje ya yi watsi da shawarar Sarkin Musulmi kan muƙabala

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da matsayar da Jama’atu Nasril Islam bisa jagorancin Sarkin Musulmi ta ɗauka kan shirin muƙabalar malamai a Kano.

Da yaje zanta wa da Freedom Radio Kwamishinan al’amuran addini na Kano Dr. Muhammad Tahar Adamu Baba Impossible ya ce, basu samu saƙon Nasril Islam ba.

Ya ce, “Yadda kowa ya ke ji muma haka muka ji, kuma mu ba a ƙarƙashin ƙungiyar mu ke ba, wannan zama yana nan daram”.

Dangane da cewa zaman tuhuma za a yi ba Muƙabala ba, Baba Impossible ya ce, ba tuhuma ko husuma ce, ko kuma rigima aka kira ta sai an yi wannan zama.

Impossible ya ce, tuni shirye-shirye sun yi nisa lokaci kawai ake jira domin a fafata.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?